Bai kamata mu bari a bizne Ajimobi a cikin gidansa ba – Gwamna Makinde
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce gwamnatinsa ta yi watsi da dokokin kasa wajen bada dama a bizne tsohon gwamna Abiola Ajimobi a cikin gidansa da ke unguwar Oluyole.
Sanata Abiola Ajimobi ya rasu ne a makon da ya gabata bayan ya yi ta fama da cutar COVID-19.
Bolaji Tunji wanda ya kasance mai ba gwamnan shawara a lokacin rayuwarsa, ya ce an dakatar da bizne Abiola Ajimobi a ranar Juma’a ne bayan an tuntubi gwamnonin Legas da jihar Oyo.
A wani jawabi da gwamnatin Oyo ta fitar ta bakin hadimin gwamnan jihar, Taiwo Adisa, ta ce babu hannunta a jinkirin da aka samu.
Taiwo Adisa ya ce iyalin marigayin sun nemi a bizne shi a wani fili da ke unguwar Agodi GRA, amma gwamnati ta ki amincewa da wannan bukata saboda ana shari’a a kan wannan fili.
Amma a karshe hadimin gwamnan ya ce gwamnati ta bada damar a bizne Ajimoni a gidansa duk da hakan ya ci karo da dokokin jihar.
“A dalilin yawan tambayoyin da ake samu daga gidajen yada labarai game da jinkirin da aka samu wajen bizne tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, gwamnati ta na shaida cewa babu burbushin gaskiya a rade-radin da ke yawo cewa gwamnati ta jawo aka bata lokaci wajen jana’iza.”
KU KARANTA: Abin da ya hana a rufe Ajimobi kwanaki bayan ya mutu a asibiti
“Jita-jitar da ake yadawa su na kokarin bata sunan gwamnatin jihar Oyo ne, tare da siyasantar da mutuwar, ya samu karbuwa a sauran gidajen yada labarai bayan an fara rade-radin a kafafen sada zumunta na zamani.”
Hadimin Seyi Makinde ya ce an tuntubesu a ranar Asabar game da labaran da su ka cika gari.
“Bari ayi jawabi da babbar murya cewa gwamna Injiniya Seyi Makinde bai da hannu ko kadan a jinkirin da aka samu wajen bizne Sanata Ajimobi.”
“Iyalin mamacin ta hannun wani, sun tuntubi gwamnatin jihar ta bada damar a bizne tsohon gwamnan a wani fili a Agodi GRA, wanda ake shari’a a kansa. Kuma shi Ajimobi ne ya shiga kotu a kan filin.”
“Dole ta sa gwamna Seyi Makinde ya ki amincewa da wannan bukata.”
“Gwama Makinde ya yi watsi da dokar kasa ta jihar Oyo, ya amince a bizne tsohon gwamnan a gidansa da ke unguwar Oluyole."
Makinde ya ce ba a sanar da gwamnatinsa yadda ya kamata game da batun rashin lafiya da mutuwar Ajimobi ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng