COVID-19: 'Yan sanda sun rufe hanyoyin shiga unguwar su Shehu Sani a Kaduna

COVID-19: 'Yan sanda sun rufe hanyoyin shiga unguwar su Shehu Sani a Kaduna

- 'Yan sanda a jihar Kaduna sun datse hanyoyin shiga layin su Sanata Shehu Sani a unguwar Sarki Kaduna

- 'Yan sandan sun rufe hanyoyin shiga layin ne sakamakon rasuwar wani fitaccen dan kasuwa da ke gida a layin

- Ana zargin cewa cutar coronavirus ce ta yi sanadin mutuwar dan kasuwar mai suna Shehu Usman

Jami'an Rundunar 'Yan sanda a jihar Kaduna sun rufe Layin Ahman Pategi daura da Abbas Road a unguwar Sarki Kaduna bayan wani fitaccen dan kasuwa Shehu Usman ya rasu sakamakon rashin lafiya da ake zargin coronavirus ce.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa gawar marigayin tana nan a asibitin Saint Gerald da ke Kaduna kuma har yanzu ba a bawa iyalansa gawar ba.

COVID-19: 'Yan sanda sun rufe hanyoyin shiga unguwar su Shehu Sani a Kaduna
COVID-19: 'Yan sanda sun rufe hanyoyin shiga unguwar su Shehu Sani a Kaduna. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Bidiyon wani mutum da mace suna lalata a kan titi cikin motar UN ya jawo cece-kuce

Wakilin majiyar Legit.ng kuma ya ruwaito cewa a kalla yan sanda 12 sun rufe hanyoyin shiga layin da gidan dan kasuwar ya ke.

An gano cewar a layin akwai gidajen manyan mutane da suka hada da Sanata Shehu Sani, Umaru Mutallab, Mahe Dange, jigo a jamiyyar D kuma dan takarar kujerar sanata a jihar Sokoto.

Har wa yau, wani babban dan kasuwa, Mahdi Shehu, Mai Dialogue plaza, shima yana da gida a layin.

A wani labarin, kun ji cewa an birne gawar tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi a ranar Lahadi a garin Ibadan babban birnin jihar Oyo.

An yi wa Ajimobi jana'iza irin ta koyarwar addinin musulunci sannan aka birne shi a gidansa da ke 6th Avenue, Yemoja Street, Oluyole Estate, Ibadan cikin yanayi na tsaro kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamnatin jihar ta Oyo ta ki amincewa a birne marigayin a gidansa da ke Agodi GRA saboda ana shariar a kotu game da gidan duk da cewa nan iyalansa suka fi so.

An birne tsohon shugaban riko na jami'yyar All Progressives Congress, APC, mai mulki misalin karfe 10:05 na safe.

Ajimobi, mai shekaru 7 a duniya ya rasu ne a wani asibiti da ke Legas.

Rahotanni sun ce an bi dukkan dokokin birne wadanda suka mutu sakamakon cutar coronavirus yayin janai'zarsa.

Mutanen da suka hallarci jana'izar ba su kai 2 ba cikinsu har da matar tsohon gwamnan, Cif Florence Ajimobi da wasu daga cikin iyalansa na yan uwansa na kusa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel