Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun mamaye gidan marigayi Ajimobi

Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun mamaye gidan marigayi Ajimobi

Rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta tura jami'anta gidan marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi.

Gwamnatin jihar bata amince da inda iyalansa suka zaba don binne mamacin ba.

A lamarin lokacin da jaridar The Nation ya ziyarci wurin, ta samu motar 'yan sanda biyu, motar sintiri daya da kuma wata mota kirar Kia Rio wacce jami'an tsaron farin kaya suka ajiye a kusa da wurin.

Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun mamaye gidan marigayi Ajimobi
Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun mamaye gidan marigayi Ajimobi Hoto: The Nation
Asali: Depositphotos

Wasu majiyoyi sun ce tura jami'an tsaro da aka yi don mamaye wurin baya rasa nasaba da rigimar da ake kan wurin da iyalan mariayi tsohon gwamnan suka zaba domin binne shi.

Majiyoyi da dama sun kara da cewa, akwai yuwuwar an tura jami'an tsaron ne saboda a kiyaye dokoki ko kuma ta yuwu suna wurin ne koda iyalan mamacin za su matsa binne shi a wurin.

KU KARANTA KUMA: Buratai: Ba za mu huta ba sai mun tabbatar da tsaron kowa a kasar nan

Kokarin zantawa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi ya tashi a tutar babu.

An tura mishi sakonnin karta kwana amma har yanzu babu amsa.

A ranar Alhamis ta makon da ya gabata ne, dai Abiola Ajimobi ya amsa kiran mahaliccinsa a wani Asibiti a jihar Legas bayan fama da cutar korona.

Sai dai kuma har zuwa yau Lahadi, 28 ga watan Yuni, ba a binne tsohon gwamnan ba sakamakon rashin cimma matsaya tsakanin gwamnatin jihar da iyalansa a kan wurin da za a binne gawarsa.

Hakazalika wasu al’ummar Musulmi sun yi gargadi a kan shirin iyalan tsohon gwamnan jihar Oyo na binne shi a cikin masallaci.

A baya bayan ne dai kakakinsa, Bola Tunji, ya sanar da cewa a za binne shi a babban masallacinsa da ke Oke-Ado a garin Ibadan, babban birnin jihar a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuni da karfe 12.00 na rana.

Wannan sanarwa ta tayar da kura yayin da wasu al'ummar musulmi suka tabbatar da haramcin yunkurin bisa ga madogara ta shari'ar Musulunci.

An tattaro cewa Musulmai a fadin Najeriya sun ce abinda iyalan marigayin ke kokarin yi na binneshi cikin Masallaci Haramun ne kuma hakan zai sa mutane su daina Sallah a Masallacin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel