Jana'izar Ajimobi: Hadiminsa ya bayyana yadda za ta kasance
Iyalan marigayi tsohon gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi sun sanar da cewa za a birne shi ne ranar 28 ga watan Yuni bayan anyi masa salla a masallacin Sanata Ishaq Abiola Ajimobi da ke Oke-Ado, Ibadan da karfe 12 na rana.
Mai magana da yawun marigayin, Bolaji Tunji ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Jumaa.
Mr Tunji ya ce iyalan mamacin da gwamnatocin jihohin Legas da Oyo ne suka tsara yadda za a birne shi.
Jana'izar Ajimobi za a yi ta ne a tsakanin iyalansa, iyalan marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo suka sanar kamar yadda dokokin dakile yaduwar cutar coronavirus take.
Tunji ya sanar da manema labarai hakan a garin Ibadan. Ya ce ba za a yi jana'izar ba a ranar Juma'a ba, kuma iyalansa kadai za su halarta.
Ya kara da cewa za a sanar da shirye-shiryen jana'izar daga baya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ajimobi ya rasu a ranar Alhamis a jihar Legas a asibitin First Cardiologist Consultant, asibitin kudi da ke jihar Legas.
Kwamishinan lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi ya rasu sakamakon cutar coronavirus da ta kama shi.
KU KARANTA: Kaduna: 'Yan sintiri sun kashe matashi mai shekaru 17 - 'Yan sanda
Legit.ng ta gano cewa Tunji ya sanar da cewa za a yi jana'izar ne ba tare da taron jama'a ba kuma cike da kiyaye dokokin hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC).
"Nan babu dadewa za a sanar da shirye-shiryen jana'izarsa amma za a kiyaye dokokin hukumar kula da cututtuka masu yaduwa (NCDC)," yace.
Ya yi kira ga masu zaman makoki da ke zuwa gidan mamacin da su kiyaye dokokin NCDC ta hanyar wanke hannu, saka takunkumin fuska da yin nesa-nesa da juna.
Ajimobi ya rasu ne a wata asibiti mai zaman kanta da ke jihar Legas a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni yayin da yake da shekaru 70 a duniya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng