Magu ya bayyana kasar Afrika da mabarnata dukiyar Najeriya suka mayar gida

Magu ya bayyana kasar Afrika da mabarnata dukiyar Najeriya suka mayar gida

Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC), ya ce mutanen da ake tuhuma da barnatar da dukiyar Najeriya sun mayar da kasar Ghana wurin buya.

Da yake magana da manema labarai ranar Juma'a a Abuja, Magu ya bayyana cewa EFCC ta fara shirin dira kasar Ghana domin cafko irin wadannan mutane tare da kwace dumbin kadarar da suka boye a kasar.

Magu ya bayyana hakan ne yayin da tawagar wasu kwararru daga cibiyar kula da tattalin dukiyar jama'a da dimokradiyya (CIPRMP) suka ziyarce shi a ofishinsa da ke hedikwatar EFCC a Abuja.

A cewarsa, EFCC ta hada kai da takwararta a Ghana domin fara aikin kwato kadarorin da mabarnata daga Najeriya suka mallaka a kasar.

"Babu ruwan cin hanci da iyakokin kasashe, laifi ne da ke shiga kasa - kasa. Mu na shirin yadda za mu shiga Ghana domin fara kwato kadarorinmu da aka boye a kasar.

Magu ya bayyana kasar Afrika da mabarnata dukiyar Najeriya suka mayar gida
Ibrahim Magu
Asali: UGC

"Mu na kira ga 'yan Najeriya da su bawa EFCC hadin kai ta hanyar sanar da ita muhimman bayanai da zasu taimaka mata a aikin da za ta fara a kasar Ghana.

DUBA WANNAN: Sule Lamido ya ci gyaran Atiku a kan kalaman yabon jam'iyyar PDP

"Akwai mabarnata da yawa da ke boye a Ghana. Tuni mun fara tattaunawa a kan dawo da su gida tare da dukiyar da suka boye a can," a cewar Magu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel