Maigidana yana shayar da 'ya'yana giya - Matar aure
Wata kotun gargajiya da ke Ibadan ta kashe auren shekaru biyar a ranar Juma'a bayan ta tabbatar da cewa mijin na shayar da 'ya'yansa giya.
Matar mai suna Mufuliat Soremekun, ta sanar da cewa mijinta na shayar da 'ya'yansu giya, jaridar The Nation ta wallafa.
A koken da ta kai, Soremekun wacce madinkiya ce, ta sanar da kotun cewa ta hakura da auren saboda mijinta ya yanke shawarar mayar da 'ya'yanta biyu mashayan giya.
Alkalin kotun, Ademola Odunade, wanda ya jagoranci sauran alkalan biyu, Alhaji Suleiman Apanpa da Alhaji Rafiu Raji, ya tsinke igiyar auren babu ja'in'ja.
Odunade ya bai wa mai korafin rikon yaran tare da bai wa wanda ake karar umarnin biyanta N10,000 na ciyar da yara. Zai dauka dawainiyar karatunsu tare da sauran walwala.
Ya shawarci masoya masu fatan kasancewa tare da juna har abada, da su yi babban bincike a kan abokan soyayyarsu kafin su yi aure.
Tunda farko, mai korafin ta zargi mijinta da zama mashayi kuma rigimamme.
"Na gaji da yi wa Abas magana a kan shan giyar da yake yi, wanda ya gada ne daga mahaifinsa. Na kamu da hawan jini saboda matsalarsa.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Yadda 'yan fashi suka bindige dan uwansu har lahira yayin sata
"Abu mafi muni shine yadda Abas ke shayar da 'ya'yana giya. Daya shekararsa hudu dayan kuwa bai kai haka ba," Mufuliat tace.
Ta zargin mijin nata da yi mata karya a kan yanayin kwayar halitattarsa. "Na sanar da Abas cewa yanayin kwayar halittata AS ne amma sai yace min shi AA ne.
"Daga bisani na gane cewa AS ne kamar ni," ta zarga.
Bayan karanta karar, wanda ake kara ya musanta dukkan zargin da ake masa inda ya kwatanta matarsa da barauniya.
Abas ya ce matarsa ta balle masa asusunsa a gida inda ta kwashe masa har N80,000.
"Da gaske wani lokacin ina dukan Mufuliat amma sau da yawa saboda bata min biyayya ne.
"Mufuliat da 'yan uwanta sun tatseni tsaf kuma yanzu ana bina tarin bashi saboda kokarin birgesu da nayi
"A takaice, ta yi min karyar tana dauke da ciki na uku. Ta san ina bata kudi mai tarin yawa idan ta samu ciki. Na yi mata komai amma kullum bata fadin alheri a kaina," Abas ya yi bayani.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng