NDLEA ta bankado wasu batagari da ke sayar da 'hodar iblis' a Kano

NDLEA ta bankado wasu batagari da ke sayar da 'hodar iblis' a Kano

- An samu karuwar amfani da safarar miyagun kwayoyi a Kano bayan an saka dokar kulle, a cewar hukumar NDLEA

- Kwamandan NDLEA a jihar Kano, Dakta Ibrahim Abdul, ya ce sun samu nasarar kama miyagun kwayoyi da nauyinsu ya kai kilogram 7,873,937

- Ya kara da cewa NDLEA reshen jihar Kano ta kama mata 16 daga cikin jimillar mutane 565 da ake zargi da laifin sha da safarar miyagun kwayoyi

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Kano ta ce an samu karuwar yawaitar amfani da kayan maye a jihar tun bayan saka dokar kulle saboda bullar annobar korona.

Kwamandan NDLEA a jihar Kano, Dakta Ibrahim Abdul, ne ya sanar da hakan yayin da ya ke magana da manema labarai a wurin taron ranar nuna kyama a kan amfani da safarar miyagun kwayoyi ta duniya wanda ake gudanarwa ranar 26 ga watan Yuni na kowacce shekara.

Abdul ya ce NDLEA ta samu nasarar kama miyagun kwayoyi da nauyinsu ya kai kilogram 7,873,937.

Ya ce NDLEA ta kama miyagun kwayoyi da nauyinnsu ya kai ton 1.2 wadanda suka hada da kwayoyi masu birkita kwakwalwa da nauyinsu ya kai kilogram 4,374.629 da hodar iblis mai nauyin kiogram 80.

NDLEA ta bankado wasu batagari da ke sayar da 'hodar iblis' a Kano
Jami'an NDLEA
Asali: UGC

"Wata babbar nasara da muka samu ita ce ta gano wasu manyan dilolin hodar iblis da jami'anmu suka yi, mun kama mace daya da wani namiji daya, mun kamasu da hodar iblis da nauyinta ya kai 100gm," a cewar Abdul.

DUBA WANNAN: Sule Lamido ya ci gyaran Atiku a kan kalaman yabon jam'iyyar PDP

Abdul ya kara da cewa jami'an NDLEA sun kama wata mota dauke da tabar wiwi da nauyinta ya kai 283kg.

Ya ce an kama motar ne a karamar hukumar Wudil yayin da take kan hanyarta ta zuwa jihar Bauchi.

Kazalika, ya bayyana cewa jami'an NDLEA sun sake samun nasarar kama wata mota dauke da tabar wiwi mai nauyin 223kg a kan titin Kano zuwa Zaria.

Ya kara da cewa NDLEA reshen jihar Kano ta kama mata 16 daga cikin jimillar mutane 565 da ake zargi da laifin sha da safarar miyagun kwayoyi.

Kwamandan ya ce suna fuskantar matsalar karancin jami'ai, motocin zirga - zirga, da sauran kayan aiki, musamman na bawa ma su shaye - shaye horon gyaran tarbiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel