Oyo: Gwaji ya nuna ina dauke da kwayar COVID-19 – Inji Seun Fakorede

Oyo: Gwaji ya nuna ina dauke da kwayar COVID-19 – Inji Seun Fakorede

Kwamishinan harkokin wasanni da cigaban matasa na jihar Oyo, Mista Seun Fakorede ya kamu da mummunar cutar nan ta COVID-19.

An gano cewa Seun Fakorede ya na dauke da Coronavirus bayan an yi masa gwaji. Yanzu haka kwamishinan ya killace kansa domin gudun yadawa jama’a wannan cuta.

Fakorede mai shekaru 28 da haihuwa shi ne ‘dan auta a gwamnatin jihar Oyo, kuma ya na cikin matasan da ke rike da kujerar kwamishina a Najeriya.

A cewar Fakorede, duk da bai san inda ya dauko cutar ba domin ya na yin kaffa-kaffa wajen bin dokokin lafiya, yanzu ya dauki matakan kare sauran mutane.

Seun Fakorede ya shaidawa jaridar Punch cewa har zuwa safiyar ranar Juma’a, 26 ga watan Yuni, 2020, ba ya jin wata alamar rashin lafiya, ya ce cutar ba ta nuna a jikinsa ba.

Kwamishinan wasannin ya ce ta kamata a sani cewa wannan cuta ta COVID-19 ba mutuwa ba ce, domin har mai gidansa, gwamna Seyi Makinde ya yi fama da cutar, kuma ya warke.

KU KARANTA: Yadda Ajimobi ya kamu da cuta bayan ya je taron APC a Abuja

Oyo: Gwaji ya nuna ina dauke da kwayar COVID-19 – Inji Seun Fakorede
Seun Fakorede
Asali: Twitter

“Gwaji ya nuna ina dauke da kwayar cutar COVID-19, kuma ina so in sanar da ku cewa babu wani dalilin tada hankali domin ina nan garau cikin koshin lafiya.” Inji sa.

Mai girma kwamishinan ya kara da cewa: “Ina da lafiya ba tare da jin akwai wasu alamun cuta a jiki na ba, ko in kai ga fadi kasa.”

“Kafin sakamakon gwajin ya fito, ban taba tunani ko da wasa cewa zai nuna ina dauke da cutar COVID-19 ba. Na fadi haka ne saboda duk da aikin da ke gabana, ina yin taka-tsan-tsan tun da annobar COVID-19 ta shigo Duniya.”

Ya kara da cewa: “Na yi gwajin kamar sauran mutane, ba tare da tsoron komai ba. Babu wata alamar rashin lafiya a jiki na. Yanzu kuma har gobe ba na jin tsoron komai.”

A jiya Alhamis mu ka samu labarin cewa tsohon gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi ya mutu bayan ya yi kwana da kwanaki ya na famar jinyar cutar Coronavirus a wani asibitin Legas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel