Lokacin mayar da dokar hana fita ya yi - Sakataren gwamnatin tarayya

Lokacin mayar da dokar hana fita ya yi - Sakataren gwamnatin tarayya

Yayinda adadin sabbin mutanen da ke kamuwa da cutar Korona ta karu a Najeriya, kwamitin yaki da cutar ta fadar shugaban kasa PTF ta ce lokaci ya yi da za'a mayar da dokar hana fita.

Za ku tuna cewa lokacin da cutar Korona ta barke a Najeriya, gwamnatin tarayya ta kakaba dokar hana fita a jihohin Legas, Ogun da birnin tarayya Abuja na tsawon makonni biyar domin takaita yaduwar cutar

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin ya bayyana yiwuwar sake sanya dokar jiya yayin hirar kwamitin da manema labarai a Abuja

Ya nuna bacin ransa yadda yan Najeriya ke yiwa cutar rikon sakainar kashi.

Yace: "Shin kun san gaskiyar magana? Da ina da iko, lokacin mayar da dokar kulle yayi. Dokar hana fitar ba abu bane da dadi amma lokacin mayarwa yayi saboda yadda naga mutane na yiwa abin rikon sakainar kashi."

Lokacin mayar da dokar hana fita ya yi - Sakataren gwamnatin tarayya
Sakataren gwamnatin tarayya
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamna da matarsa sun killace kansu bayan diyarsu ta kamu da cutar Korona

Yayinda yake kira ga yan Najeriya su dau abin da gaske, Boss Mustapha ya cewa mutane su mayar da hankali wajen bin shawari da ka'idojin hukumar.

"Na ga yadda ake wasa da COVID-19 a yau. Mutane na yi kamar abin ta wuce. Wannan ba abin wasa bane kuma ina kira ga yan Najeriya masu sauraron mu cewa; mu dau abin nan da gaske."

"Kawo yanzu da mutane 500 suka mutu, ba zaka jahilci abin ba, ba zai yiwu kace baka san ko mutum daya da ya kamu da cutar ba." Yace

Ya ce sun gano har yanzu mutane da dama basu yarda akwai cutar ba shi yasa ake kin bin dokoki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel