Bidiyo: Yadda Dino Melaye ya rera wakar 'ba'a' ga Oshiomhole

Bidiyo: Yadda Dino Melaye ya rera wakar 'ba'a' ga Oshiomhole

Sanata Dino Melaye ya wallafa wani bidiyonsa sabo inda yake kwasar nishadi tare da yi wa dakataccen shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole ba'a.

Tsohon dan majalisar ya rera baitukan wakarsa a harshen Yarbanci mai cike da habaici duk don tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, a ranar 25 ga watan Yuni.

"Me yasa Buhari da APC suka kai Oshiomhole karshe? Amma dai, ni da Sanata Saraki muna jiran shaidar murabus dinmu daga wurin 'tozartaccen' tsohon shugaban jam'iyyar APC," ya rubuta.

Idan za mu tuna, kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar APC wanda Oshiomhole ya kafa kafin a dakatar da shi, duk an warware a jiya, 25 ga watan Yuni.

Hakan ta faru ne a taron shugabannin jam'iyyar APC da aka yi a fadar shugaban kasa a Abuja.

Mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, Victor Giadem ya kira taron kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari, Farfesa Yemi Osinbajo da gwamnonin APC duk sun halarta.

KU KARANTA: Magani a gonar yaro: Magungunan cutuka 7 da Zobo ke yi ga dan Adam

A wani labari na daban, Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu, ya bayyana cewa yana da babbar matsala da tsohon gwamnan jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomhole, bayan rikicin da ya barke a jam'iyyar APC.

Shuaibu ya sanar da hakan ne bayan da gidan talabijin din Channels ya bashi masauki a matsayin bakon shirin 'siyasarmu a yau'.

Ya bayyana cewa shi bashi da wata matsala da jam'iyyar mai mulki sai dai da dakataccen shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Kamar yadda yace, "Na matukar wahala kafin ginuwar APC kuma ina ganin abin na wahalar wa. Amma abinda bana farin ciki a kai shine yadda siyasar uban gida tayi katutu a jihar Edo."

A yayin bayani a kan sabuwar jam'iyyar PDP da ya koma, ya ce tsarin jam'iyyar ko kusa ba a hada shi da APC.

"Wani abu daya da na gane a PDP shine yadda suke gaggauta shawo kan matsalarsu. Na ga abubuwa masu banbanci daga inda na fito," mataimakin Gwamnan yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel