Jirwaye: Magu ya yi martani mai zafi bayan zargin Malami

Jirwaye: Magu ya yi martani mai zafi bayan zargin Malami

- Mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ya ce babu wata barazana da za ta hana shi yin aikinsa

- Shugaban ya bayyana cewa mahandaman kasar nan na yakarsa don suna amfani da sabbin salo wurin handame kudin kasar nan

- Ya tabbatar da cewa babu wani salo da za a zo masa da shi sabo don duk wata hanyar dakile ci gaban rashawa sai ya tabbatar da ita

Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ya ce "babu wani bacin suna da barazana" da za su hana shi yaki da rashawa.

A yayin jawabi ga wakilin kungiyar 'yan jaridu ta Najeriya a babban birnin tarayya a ranar Alhamis, Magu ya ce dole ne a hana barayi satar arzikin Najeriya.

A wata takarda da hukumar ta fitar, Magu ya ce 'yan Damfara na amfani da sabon salo wurin yakarsa.

Ya ce, "Masu sata, almubazzaranci da kuma kwashe dukiyarmu ba masoyanmu bane. Dole ne mu dakatar da su. Dole ne mu dakatar da mahandama. Sai mun dakilesu ta kowacce hanya," yace.

"Yaki da rashawa ba sauki gareshi ba a yanzu kamar a baya. Barayin na amfani da sabbin salo da dabaru wurin doke wasu dokoki da tsare-tsarenmu.

"Bayan haka, akwai wasu salon mayar damu baya tare da na dauke mana hankali da suka bullo da shi don ci gaban rashawa. A garemu, ba sabbin salo bane. Muna sane da duk wani kage na 'yan damfara.

Jirwaye: Magu ya yi martani mai zafi bayan zargin Malami
Jirwaye: Magu ya yi martani mai zafi bayan zargin Malami. Hoto daga The Cable
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon motocin alfarma da ke garejin Kaftin Ahmed Musa

"Mun san bata mata suna da suke yi amma ba za mu sare ba. Za mu ci gaba da tona musu asiri tare da fallasa duk wani yunkurinsu na cin amanar kasa. Ba za mu sare ba!"

Ya ce hukumar ta matukar mayar da hankali ta yadda ba za a iya dauke mata hankali ba.

Tsokacin Magu ya zo ne kafin a yi cikakken sati da ministan shari'a Abubakar Malami, kuma Antoni janar din tarayya, ya zargesa da cin hanci.

Ministan ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saukesa saboda zarginsa da ake yi da waskar da kudaden da ya karbowa, jaridar The Cable ta ruwaito.

Daga Magu har EFCC basu yi martani a kan wannan zargin ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel