PTF: Da ina da karfin iko, sai na sake rufe Najeriya - Boss Mustapha

PTF: Da ina da karfin iko, sai na sake rufe Najeriya - Boss Mustapha

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa, Boss Mustapha a ranar Alhamis ya ce za a sake kulle Najeriya da yana da karfin ikon aikata hakan.

Mustapha ya ce duk da ba za a so komawa kullen ba, shine abinda yafi cancanta idan aka duba halayyar wasu 'yan Najeriya.

A mako mai zuwa ne ake tsammanin kwamitinsa ya mika rahoton yaki da cutar korona da suka kwashe watanni uku suna yi a gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kwamitin yaki da cutar na ci gaba da jajanta yadda 'yan Najeriya ke watsi da dokokinsu na dakile yaduwar cutar.

A yayin jawabi a taron su na ranar Alhamis, SGF ya jajanta yadda wasu jama'a ke kai wa cutar korona runguma kamar a wasan kwaikwayo.

PTF: Da ina da karfin iko, sai na sake rufe Najeriya - Boss Mustapha
PTF: Da ina da karfin iko, sai na sake rufe Najeriya - Boss Mustapha Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Kamar yadda alkakumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta bayyana na karshe, ta tabbatar da cewa mutum 22,020 ne aka samu da cutar a Najeriya yayin da rayukan 542 suka salwanta sakamakon annobar.

Mustapha ya ce: "kuna son sauraron gaskiya? Da ace ina da karfin iko, zan sake kulle kasar nan. Ba za ku so hakan ba saboda wasu na rungumar cutar kamar a wasan kwaikwayo."

KU KARANTA KUMA: Rushe shugabannin APC: Mambobin kwamitin NWC na Osiomhole sun garzaya kotu

SGF ya ce dole ne 'yan Najeriya su kiyaye dokoki don dakile yaduwar cutar cikin al'umma.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su dauka cutar da gaske tare da kiyaye dokokinta.

A wani labari na daban, kakakin majalisar jihar Kaduna, Alhaji Yusuf Zailani ya umarci dukkan ma'aikatan majalisar da masu wakilci da su mika kansu don gwajin cutar coronavirus.

Ya sanar da hakan ga manema labarai ta bakin mataimakin shugaban kwamitin lafiya na majalisar, Ali Kalat, a ranar Talata a garin Kaduna.

Kalat ya ce wannan umarnin ya zama dole bayan wani ma'aikacin majalisar ya kamu da cutar. Ya ce babu dan majalisar da ya kamu amma.

"Amma ya zama dole mu mika kanmu don gwaji don tabbatar da ingancin lafiyar dukkan 'yan majalisar.

"Kakakin majalisar ya bada wannan umarnin na cewa kowanne ma'aikaci ya garzaya gwaji," yace.

Kalat ya ce, "Bayan kammala gwajin, za mu rufe majalisa tare da sauraron umarni na gaba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel