Abun tausayi: Bidiyon masu kukan mutuwar tsohon gwamna Ajimobi a gidansa na Ibadan

Abun tausayi: Bidiyon masu kukan mutuwar tsohon gwamna Ajimobi a gidansa na Ibadan

Tsohon gwamna kuma Sanata na jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya rasu a ranar Alhamis 25 ga watan Yuni, shekarar 2020 sakamakon cutar da ake zargin COVID-19 ce; wato coronavirus.

Tsohon gwamnan ya mutu ne yana da shekaru 70 bayan fama da muguwar cutar na ta Coronavirus.

Ajimobi, ya yi gwamnan jihar Oyo tsakanin shekarar 2011 da 2019, kafin dag baya a nadashi mataimakin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC na yankin kudu.

Tsohon gwamnan ya yi jinya ne a asibitin First Cardiologist and Cardiovascular Consultants Hospital, dake Legas ranar 2 ga watan Yuni, 2020.

Daga baya ya warke daga cutar Koronar amma duk da haka bai daina jinya ba. A kwantar da shi tare da matarsa, Florence, a asibitin amma ta samu sauki kuma aka sallameta.

Kamar sauran manyan masu kudi, Ajimobi ya yi jinyar cutar a asibitin kudi maimakon cibiyar killace masu cutar na gwamnati.

Ga wasu muhimman abubuwa a kan marigayi Ajimobi:

1. An haifi Abiola Ajimobi ne a ranar 16 ga watan Disamban shekarar 1949 a Oja-Iba a Ibadan.

2. Kakansa basarake na Sobaloju na Ibadan. Mahaifinsa, Pa Ajimobi, shima dan majalisa ne a tsohuwar shiyar Yamma kuma kawunsa, Hon. N.A. Ajimobi tsohon ministan Ayyuka da Sufuri ne a shiyar ta Yamma.

3. Yayi karatunsa na frimari a Saint Patricks School, Oke-Padre kuma ya kammala frimari a City Council Primary School Aperin.

Ya yi karatun sakandare a Lagelu Grammar School. Yana cikin dalibai masu hazaka wurin wasanni kamar kwallon kafa, guje-guje da sauransu.

DUBA WANNAN: Mai Mala Buni ya fadi ta hanyar da zai warware rigingimun APC

4. Ajimobi ya yi karatun digiri na farko a State University of New York a Buffalo a Amurka. Ya yi digirinsa na biyu a Governors State University, Illinois.

5. Ajimobi ya auri Florence Ajimobi a shekarar 1980 kuma sun haifi yara biyar. Diyarsa ta farko Abisola Kola-Daisi 'yar kasuwa ce wacce ta kafa kamfanin Florence H Luxury.

6. A 2003, Ajimobi ya zama Sanata a Najeriya. Ya rike mukamin mataimakin shugaban marasa rinjaye.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng