Damina: Sharudda 7 na kiyayewa yayin ambaliyar ruwa

Damina: Sharudda 7 na kiyayewa yayin ambaliyar ruwa

A yayin da yanayi na damina ke kara kamawa, babu shakka ana samun ambaliyar ruwa a wasu wurare a fadin kasar nan.

Abun takaici ne yadda ambaliyar ruwan ke sa mutane suna rasa matsuguni.

Hukumar NHISA ta ja hankalin jama'a kan cewa mazauna wasu sassan kasar nan za su iya fuskantar ambaliyar ruwa a shekarar nan saboda sauyin yanayi.

A makonni da suka gabata, ruwa mai karfi ya hargitsa wasu sassan jihar Legas da wasu jihohi.

Damina: Sharudda 7 na kiyayewa yayin ambaliyar ruwa
Damina: Sharudda 7 na kiyayewa yayin ambaliyar ruwa Hoto: The Nation
Asali: UGC

Abun takaici ne yadda ambaliyar ke lashe rayuka a wasu sassan kasar nan. Wata matashiya mai shekaru 17 mai suna Ayisat da yarinya mai shekaru 4 mai suna Azeezat sun rasa ransu sakamakon ambaliyar ruwa, The Nation ta ruwaito.

Ga wasu al'amura da ya dace a kiyaye yayin ruwa mai tsananin karfi.

1. A lokacin da aka fara ambaliya, kada a yi yawo a cikin ruwan. Ruwa mai zurfin inci 6 kacal zai iya tafiya da mutum.

2. Akwai matukar amfani idan aka guji yin wanka a ruwa ko tuka mota a yayin da ake ambaliya. Gara a zauna gida lafiya.

3. Akwai amfani idan aka kiyaye gadoji da kuma ruwa mai tafiya da Sauri. Ruwa mai tafiya zai iya yin awon gaba da jama'a ba tare da an sani ba.

4. Mafi akasarin direbobi basu damuwa da wannan amma yana da matukar hatsari – kada ka kuskura ka tuka abun hawa a yankunan da ked a ambaliyar ruwa.

Idan ambaliyar ruwa ya kai saman motarka, ka yasar da motar sannan hau wajen da ke da tudu sosai idan za ka iya hakan a tsanaki.

5. A kiyaye taba wayar wuta ko wani abu da ke aiki da lantarki idan ruwa ya taba shi.

KU KARANTA KUMA: Katsina: Jami'in tsaro da mutum shida sun rasa ransu a sabon hari

6. Idan ruwa ya cika gida, a kashe duk wata hanyar wutar lantarki. A kiyaye zama kusa da falwayar wuta a tituna.

7. Zubda shara a kwata ko hanyoyin ruwa na iya kawo toshewar hanyar da ruwa ke gudana. Hakan na iya kawo ambaliyar ruwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel