Abinda yasa nake son cire riga a fim - Jarumi Zahradeen Sani

Abinda yasa nake son cire riga a fim - Jarumi Zahradeen Sani

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Zahradeen Sani ya ce yana matukar jin dadi idan ya tube rigarsa a yayin da ake fim.

Shahararren dan fim din ya sanar da hakan ne a wata tattaunawar da yayi da BBC a Instagram a ranar Alhamis.

Ya ce tube rigarsa na da alaka da yadda yake motsa jiki, kuma tube rigar salo ne irin da tauraron Bollywood Salman Khan ke yi.

Zahradeen Sani ya ce ya fara fim a shekarar 2003 kuma fim dinsa na farko shine Makamashi.

Tauraron ya ce jarumi Ali Nuhu ne mai gidansa a masana'antar saboda shine mutum na farko da ya fara masa jagora a harkar.

Da aka tambayesa bakandamiyarsa a fina-finansa, ya ce 'Daga Ni Sai Ke' ne fim din da yafi so.

Jarumin ya ce yafi sha'awar fitowa a matsayin mugu, lamarin da yaci karo da ra'ayin sauran abokan sana'arsa.

Hakazalika, jarumin ya ce shi kwararre ne a sana'ar dinki baya da film. Ya yi murabus ne a 2004 amma yana da shagunan dinki a halin yanzu.

Jarumin ya bayyana rashin jin dadinsa game da matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewacin Najeriya.

Abinda yasa nake son cire riga a fim - Jarumi Zahradeen Sani
Abinda yasa nake son cire riga a fim - Jarumi Zahradeen Sani. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon motocin alfarma da ke garejin Kaftin Ahmed Musa

A wata hira ta daban, jaruma Surayya Aminu, wacce ake kira da Rayya a cikin shiri mai dogon Zango mai suna Kwana Casa'in na tashar Arewa24, ta ce tana fatan zama fitacciyar 'yar kasuwa.

Jarumar ta bayyana hakan ne yayin da tayi hira da BBC a shafinsu na Instagram. Duk da 'yar wasan Hausan ta ce a jihar Legas aka haifeta kimanin shekaru 21 da suka shude, ta ce a jihar Kaduna ta girma.

Surayya ta ce shahararta ya bayyana ne sakamakon fitowa da ta yi a shiri mai dogon zango na Kwana Casa'in, amma ta fara harkar fim tun watanni shida kafin nan.

"Na yi fina-finai irinsu Hanyar Arziki, Yarena, Kanin Miji da sauransu," in ji ta.

Duk da haka, ta ce tun tana karama ta ke fatan zama 'yar jarida, wanda hakan ne yasa ta fara sha'awar shiga harkar fim.

Kamar yadda Surayya ta ce, jaruminta shine Ali Nuhu a maza amma a mata Rahama Sadau da Fati Muhammad ne madubin dubawarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng