An sake rufe sakatariyar APC na kasa, an hana sakataren jam'iyyar shiga ofis

An sake rufe sakatariyar APC na kasa, an hana sakataren jam'iyyar shiga ofis

'Yan sandan da suka mamaye sakatariyar jami'yyar APC na kasa sun hana sakataren jamiyyar Arc Waziri Bulama shiga ofishinsa da ke cikin sakatariyar.

'Yan sandan dauke da bindigu da suka iso majalisar tunda safe cikin mota kirar Toyata Land Cruiser mai lamba Abj-140DN ne suka dakatar da Bulama.

Cikin mamaki, Bulama ya nemi ganin shugaban tawagar 'yan sandan kana daga bisani ya kira kwamishinan 'yan sanda na Abuja.

Ya shaidawa manema labarai cewa, "Na iso aiki da safe na tarar da yan sanda da suka ce an basu umurni daga sama su rufe sakatariyar.

"Na kira kwamishinan 'yan sanda inda ya ce zai aiko da wani babban jamii don ya duba abinda ke faruwa.

"Maaikatan sakatariyar suna yi wa mambobin mu fiye da miliyan 16 da ke fadin kasar nan hidima. Kamar maaikatan gwamnati suke."

Yanzu-yanzu: An sake rufe sakatariyar APC na kasa
Yanzu-yanzu: An sake rufe sakatariyar APC na kasa. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump

Tunda farko, mun kawo muku cewa jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun sake rufe sakatariyar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa da ke Abuja.

Tun misalin karfe 9 na safiyar yau Alhamis ne wasu manyan motoci kirar hilus da Peugeot 604 suka isa harabar sakatariyar kuma suka zagaye ta.

An umurci ma'aiakatan jam'iyyar da suka iso aiki da wuri su fice daga ofisoshinsu.

The Nation ta ruwaito cewa Sufeta Janar na Rundunar Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ne ya bayar da umurnin rufe sakatariyar.

An umurci Kwamishinan 'yan sanda na birin tarayya Abuja ya tabbata babu wanda ya shiga cikin harabar sakatariyar.

Kwamitin gudanar da jam'iyyar, NWC, karkashin jagorancin Hon. Victor Giadom a ranar Talata sun samu amincewar shugaban kasa su kira taron Kwamitin masu zartarwa, NEC, da za a gudanar ta intanet.

Amma 'yan jam'iyyar masu goyon bayan Sanata Abiola Ajimobi sun nuna rashin amincewarsu da kiran taron ta NEC da suka ce ya saba wa dokokin jam'iyyar.

Sun ce ba za su hallarci taron ta NEC ba duk da cewa ana sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai hallarci taron daga fadarsa ta Aso Rock ta yanar gizo wata intanet.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel