Zaben fidda gwani na PDP: Gwamnan Bauchi ya dira jihar Edo

Zaben fidda gwani na PDP: Gwamnan Bauchi ya dira jihar Edo

A yayin da jami'yyar Peoples Democratic Party’s, PDP, ke shirin fara gudanar da zaben fidda dan takarar gwamna a jihar Edo a yau Alhamis, wasu jiga jigan jami'yyar sun fara isa jihar don hallatartar taron.

Cikin wadanda suka isa jihar ta Edo har da Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed wanda ya isa jihar a daren jiya Laraba 24 ga watan Yunin 2020 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Da farko an shirya yin zaben ne a ranar 19 ga watan Yunin, sannan daga bisani aka dage zuwa ranar 23 kuma daga karshe aka tsayar da ranar 25 ga watan Yuni.

Zaben fidda gwani na PDP: Gwamnan Bauchi ya dira jihar Edo
Zaben fidda gwani na PDP: Gwamnan Bauchi ya dira jihar Edo. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Bidiyon yadda wani dan Najeriya da ya diro daga bene hawa 9 kuma bai mutu ba

Ana sa ran wakilai 2,229 ne za su kada kuriunsu a zaben da zai fitar da dan takarar gwamna na jami'yyar da zai fafata a zaben da za ayi a ranar 19 ga watan Satumba.

Sakataren Watsa Labarai na kasa na PDP, Kola Ologbondiyan ya ce jami'yyar ta bi dokoki wurin zaban wakilan da za su kada kuria don fitar da dan takarar jami'yyar.

Da farko mutum hudu ne suka siya fom din shiga takarar kuma an tantance su don fafatawa a zaben.

Baya ga Gwamna Godwin Obaseki, sauran yan takarar sun hada da Gideon Ikhine, Ogbeide-Ihama da Kenneth Imasuagbon.

Rahotanni sun ce biyu daga cikin yan takarar sun janye wa Obaseki.

A baya, Legit.ng ta ruwaito muku cewa Obaseki ya fice daga jami'yyar APC ne bayan hana shi shiga takarar zaben fidda gwani ya koma PDP.

Wanda ya lashe zaben fid da gwanin na yau zai fafata da dan takarar jami'yyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu a zaben da za ayi a ranar 19 ga watan Satumba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel