Daga karshe: Kotu ta sa ranar yanke hukunci a kan kisan 'yan shi'a

Daga karshe: Kotu ta sa ranar yanke hukunci a kan kisan 'yan shi'a

- Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta saka ranar 29 ga watan Yuni don yanke hukunci a kan kisan 'yan shi'a uku da ake zargin jami'an 'yan sanda da yi

- Alkali Taiwo Taiwo a ranar Laraba ya dage sauraron shari'ar bayan kammala ji da yayi daga bakin lauyoyi

- Said Haruna, dan uwan wani dan shi'a ne ya shigar da karar inda ya zargi dan sanda da kashe dan uwansa

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta saka ranar 29 ga watan Yuni don yanke hukunci a kan kisan 'yan shi'a uku da jami'an 'yan sanda suka yi.

Mai shari'a Taiwo Taiwo a ranar Laraba ya dage sauraron shari'ar bayan kammala ji da yayi daga bakin lauyoyi.

Mai shari'ar ya saka ranar 30 ga watan Yuni don sauraron karar da wani Said Haruna, dan uwan wani dan shi'a ya shigar a kan zargin dan sanda da kashe dan uwansa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Daga karshe: Kotu ta sa ranar yanke hukunci a kan kisan 'yan shi'a
Daga karshe: Kotu ta sa ranar yanke hukunci a kan kisan 'yan shi'a Hoto: Thisdaylive
Asali: Twitter

A karar da 'yan uwan mamatan: Ibrahim Abdullahi, Ahmad Musa, Yusuf Faska da Said Haruna suka shigar, sun bukaci a bada gawar Suleiman Shehu, Mahdi Musa, Bilyaminu Abubakar Faska da Askari Hassan.

An zargi jami'an 'yan sandan Najeriya da kashesu yayin da aka mika gawarsu ma'adanar gawawwaki da ke asibitin kasa a ranar 22 ga watan Yulin 2019.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Akwai yuwuwar APC ba za ta fito takara ba a zaben Ondo - INEC

An kashesu yayin zanga-zangar lumana inda suke bukatar sakin shugabansu El-Zakzaky da matarsa.

A wani labari na daban, mun ji cewa wani makwabcin Bala Hamisu wanda aka fi sani da Wadume, mai suna Aminu Ahmed, ya ce dakarun da ke karkashin Kaftin Tijjani Balarabe sun kashe 'yan sanda uku da farar hula biyu don samun kubutar da Wadume daga hannun IRT.

Ahmed dan asalin garin Ibbi ne da ke jihar Taraba. Ya ce ya tabbatar da cewa Wadume ya shiga harkar garkuwa da mutane tun kafin jami'an tsaro su kama shi.

Dan shekaru 22 ya ce abokan Wadume da wani yayansa mai suna Awolu sun yi iyakar kokarinsu don samun sassauci ga shahararren mai garkuwa da mutanen.

A wata takarda da Ahmed yasa hannu a ranar 22 ga watan Augusta a garin Abuja, ya bayyana cewa kamen Wadume ya biyo bayan garkuwa da manyan masu kudi da kuma 'yan siyasa da ya fara yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel