Mataimakin Obaseki ya bayyana babbar matsalar da ke tsakaninsa da Oshiomhole

Mataimakin Obaseki ya bayyana babbar matsalar da ke tsakaninsa da Oshiomhole

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu, ya bayyana cewa yana da babbar matsala da tsohon gwamnan jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomhole, bayan rikicin da ya barke a jam'iyyar APC.

Shuaibu ya sanar da hakan ne bayan da gidan talabijin din Channels ya bashi masauki a matsayin bakon shirin 'siyasarmu a yau'.

Ya bayyana cewa shi bashi da wata matsala da jam'iyyar mai mulki sai dai da dakataccen shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Kamar yadda yace, "Na matukar wahala kafin ginuwar APC kuma ina ganin abin na wahalar wa. Amma abinda bana farin ciki a kai shine yadda siyasar uban gida tayi katutu a jihar Edo."

A yayin bayani a kan sabuwar jam'iyyar PDP da ya koma, ya ce tsarin jam'iyyar ko kusa ba a hada shi da APC.

"Wani abu daya da na gane a PDP shine yadda suke gaggauta shawo kan matsalarsu. Na ga abubuwa masu banbanci daga inda na fito," mataimakin Gwamnan yace.

KU KARANTA: An kama sojan da ya yi wa Buratai da shugabannin tsaro kaca-kaca

A wani labari na daban, jaridar Daily Trust ta ce wasu daga cikin jagororin da aka kafa jam’iyyar APC da su a Najeriya, sun goyi bayan taron majalisar NEC da aka kira a yau Alhamis, 25 ga watan Yuni, 2020.

Jagororin jam’iyyar APC da su ka sa hannu a wannan jawabi da ya nuna goyon bayansu da amsa goron gayyatar wannan taro sun hada da Salihu Mustapha, Polycap Udah, Capt Bala Jibrin, Ray Morphy, da Umar Kachalla Zubair.

Sauran wadanda za su halarci taron majalisar zartarwar su ne: Dr Slyvanus Amechi, Shaba Emangi, Emeka Enechi, Charles Idahosa, Mohammed Aboki Mahmud. Sai kuma Prince Maxkor Shaka Momodu da Yusuf Omobeni.

‘Ya ‘yan jam’iyyar sun yi kira ga duk wadanda ke cikin majalisar NEC, su ajiye bambancin ra’ayi a gefe, su halarci wannan muhimmin taro domin ceto jam’iyyar daga cikin halin da ta samu kanta.

Ga abin da jawabin ya ce: "Mu a matsayinmu na wakilan wadanda aka kafa jam’iyyar APC da su daga tsofaffin jam’iyyun da su ka narke, mu na murna hannu biyu-biyu da taron NEC da aka shirya za a yi a ranar 25 ga watan Yuni 2020 domin a ceci jam’iyyar.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel