'Dukkan yabo ya tabbata ga Allah': Sabon shugaban APC ya yi martani bayan samun goyon bayan Buhari

'Dukkan yabo ya tabbata ga Allah': Sabon shugaban APC ya yi martani bayan samun goyon bayan Buhari

Victor Giadom, mataimakin sakataren jam'iyyar APC, ya bayyana jin dadinsa a kan samun goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, domin kasancewa shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya sanar da cewa shugaba Buhari ya goyi bayan Giadom a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya.

A cewar Garba Shehu, shugaba Buhari zai halarci taron masu ruwa da tsaki a gudanar da harkokin APC a karkashin jagorancin Giadom.

Za a yi taron ne ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni, a fadar shugaban kasa da ke Abuja domin warware rigingimun kabilanci da APC ta fada ciki tun bayan tabbatar da dakatar da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

"Shugaba Buhari ya amince da Giadom a matsayin shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC bayan ya saurari shawarwarin masana shari'a. Shugaba Buhari ba zai yi wani abu da ya ci karo da doka ba, a saboda haka zai halarci taron jam'iyya da za a yi ranar Alhamis a karkashin jagorancin Giadom," a cewar Garba Shehu.

Da yake mayar da martani bayan sanarwar da Garba Shehu ya fitar, Giadom ya ce kasancewarsa shugaban riko na APC alheri ne ga jam'iyya.

'Dukkan yabo ya tabbata ga Allah': Sabon shugaban APC ya yi martani bayan samun goyon bayan Buhari
Victor Giadom
Asali: UGC

Jam'iyyar APC ta fada cikin rigingimun shugabanci bayan wata kotun daukaka kara ta tabbatar da dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar APC na kasa.

DUBA WANNAN: Sanatan APC daga arewa ya amince zai karbi belin Maina

Duk da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC ya sanar da sunan Abiola Ajimobi a matsayin shugaban rikon kwarya, Giadom ya yi gaban kansa wajen sanar da cewa shine halastaccen shugaban jam'iyya na rikon kwarya.

Mambobin NWC na APC sun yi watsi da Giadom tare da sanar da sunan Eta Hilliard a matsayin shugaban da zai jagoranci jam'iyyar saboda Ajimobi bashi da lafiya.

Sai dai, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da Giadom a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya duk da wata kotu da ke jihar Ribas ta dakatar da shi daga gabatar da kansa a matsayin shugaban riko na jam'iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel