Faiq Bolkiah: Tauraron Leicester City ya bayyana a matsayin ɗan kwallo mafi arziki a duniya

Faiq Bolkiah: Tauraron Leicester City ya bayyana a matsayin ɗan kwallo mafi arziki a duniya

- Faiq Bolkiah wanda ya koma Leicester City a shekarar 2016 amma har yanzu bai buga wasa ko daya ba

- Mai shekara 22 ɗan uwa ne ga Sarkin Brunei, Sultan Hassanal Bolkiah

- Faiq ya bayyana a matsayin ɗan kwallon da ya fi kowanne kudi a duniya da a yanzu ya sha gaban Ronaldo

A yayin da aka fitar da jerin 'yan kwallon da suka fi kowanne kudi a duniya, dan wasan kungiyar Leicester City, Faiq Bolkiah, ya ciri tuta inda ya sha gaban Lionel Messi da Cristiano Ronaldo.

A rahoton da jaridar kasar Spain, Marca ta fitar, ta nuna cewa, a halin yanzu Kyaftin din Argentina ko abokin hamayyarsa na Portugal, babu dayansu da ya kasance mafi arziki cikin 'yan kwallon kafa na duniya ba.

Faiq Bolkiah: Tauraron Leicester City ya bayyana a matsayin dan kwallon mafi arziki a duniya
Faiq Bolkiah: Tauraron Leicester City ya bayyana a matsayin dan kwallon mafi arziki a duniya
Asali: UGC

Faiq Bolqiah wanda ɗan uwa ne ga Sarkin Brunei, Sultan Hassanal Bolkiah, har yanzu bai bugawa kungiyar Leicester wasa ba, amma yana da tarin dukiya wadda ta kai kimanin dala biliyan 20.

Duk da cewa rahoton da jaridar Marca ta fitar bai haskaka samunsa a fannin kwallon kafa ba, sai dai an nuna cewa ya sha gaban Messi da Ronaldo cikin jerin 'yan kwallo 10 mafi arziki a yanzu.

KARANTA KUMA: Ya zama tilas a tanadi wuraren killace masu cutar korona kafin a buɗe makarantu - Adamu Adamu

Sai dai duk da hakan, Ronaldo ya sha gabana Messi yayin da ya biyo bayan Faiq a mataki na biyu, inda aka kiyasta cewa dukiyar da ya mallaka ta kai dala miliyan 460.

Ga jerin 'yan kwallon kafa 10 mafi arziki a duniya, adadin dukiyar da suka mallaka da kuma kungiyar kwallon da ta suke:

10. Paul Pogba $85m - Manchester United

9. Eden Hazard $100m - Real Madrid

8. Andres Iniesta $120m - Vissel Kobe

7. Gareth Bale (Real Madrid): $125m

6. Wayne Rooney $160m - Derby County

5. Neymar $185m - Paris Saint Germain

4. Zlatan Ibrahimovic $190m - AC Milan

3. Lionel Messi $400m - Barcelona

2. Cristiano Ronaldo $460m - Juventus

1. Faiq Bolkiah - Leicester City $20bn

Legit.ng ta ruwaito cewa, rigima ta kaure tsakanin manyan ‘yan wasan gaban kungiyar kwallon kafan Barcelona, Lionel Messi da kuma Antoine Griezmann.

Taurarin sun kaure da fada a wurin atisaye a farkon makon nan. Ana tunanin cewa ‘yan kwallon sun samu matsala ne a sakamakon wasan Sevilla na Ranar Juma’a.

Lamarin har ya kai sai da mai horas da ‘yan wasan Barcelona Quique Setien ya zo ya raba ‘yan kwallon na sa da aka dade ana rade-radin cewa ba su jituwa sosai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng