CP ya janye dukkan jami'an tsaron mataimakin gwamnan Ondo - Hadiminsa

CP ya janye dukkan jami'an tsaron mataimakin gwamnan Ondo - Hadiminsa

Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi, ya yi korafin yadda aka janye jami'an 'yan sandan da ke tsaron lafiyarsa bayan umarnin kwamishinan 'yan sandan jihar, Bolaji Salami.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar ya kasance a tsakiyar rashin jituwar da ke tsakanin gwamnan da mataimakinsa.

A ranar Asabar da ta gabata ne kwamishinan 'yan sandan jihar Ondo ya tsare mataimakin gwamnan jihar a yayin da yake kokarin fita daga gidan gwamnatin jihar da motar gidan gwamnatin, kamar yadda The Punch ta wallafa.

CP ya janye dukkan jami'an tsaron mataimakin gwamnan Ondo - Hadiminsa
CP ya janye dukkan jami'an tsaron mataimakin gwamnan Ondo - Hadiminsa. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump

A wata takarda da sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, Tope Okeowo, ya fitar a ranar Laraba, ya ce an janye masu tsaron lafiyar mataimakin gwamnan, al'amarin da zai iya jefa rayuwarsa a hatsari, iyalansa da ma'aikatansa.

Ya ce, "wannan babban al'amari ne yadda aka janye jami'an tsaron mataimakin gwamnan. Hakan zai basu damar aikata masa abinda suka ga dama.

"Shugaban kasa Muhammad Buhari, sifeta janar din 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu da darakta janar din hukumar tsaron farin kaya, Yusuf Bichi su san mummunan ci gaban da ke faruwa a jihar Ondo.

"Idan wani abu ya faru da mataimakin gwamnan, iyalansa da ma'aikatansa, a tuhumi kwamishinan 'yan sanda na jihar Ondo."

A wani martani da mai magana da yawun 'yan sandan jihar ya yi, Tee-Leo Ikoro ya musanta zargin tare da cewa babu wani shiri irin haka daga wurin kwamishinan 'yan sandan.

"Wannan zancen karya ne. Kwamishinan 'yan sanda bai da ikon janye masu tsaron lafiyar mataimakin gwamnan ba. Har yanzu mataimakin gwamna ne kuma yana da hakkin a bashi kariya," in ji shi.

A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga a jihar Katsina sun sake kai hari kauyen Unguwar Ali mai nisan kilomita 10 daga Faskari a daren ranar Talata suka kashe mutum daya tare da sace shanu fiye da 150 a cewar mazauna garin.

Kamar yadda HumAngle ta ruwaito, miyagun da adadinsu ya fi 200 sun isa kauyen a kan babura misalin karfe 11 na dare inda suka rika bi gida-gida suna neman dabobi.

Wannan harin na zuwa ne mako guda bayan wasu matasa a Katsina sunyi zanga-zanga a kan hare-haren da ake kai wa garurruwansu wadda hakan ke janyo matsaloli daban-daban.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel