An kama sojan da ya yi wa Buratai da shugabannin tsaro kaca-kaca

An kama sojan da ya yi wa Buratai da shugabannin tsaro kaca-kaca

- Hukuma ta damke wani sojan Najeriya mai mukamin Lance Corporal mai suna Martins

- An zargi sojan da fitar da wani bidiyo inda yayi wa Laftanal Janar Tukur Buratai da sauran shugabannin tsaro kaca-kaca

- Ya zargesu da nuna halin ko in kula a kan rashin tsaron kasar nan da kuma yadda 'yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka

An damke wani sojan Najeriya da ya yi wa shugaban rundunar sojin Najeriya da sauran shugabannin tsaro kaca-kaca a wani bidiyo.

A wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani, sojan mai mukamin Lance Corporal mai suna Martins, ya zargi shugaban rundunar sojin najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai da sauran shugabbanin kasar nan da rashin kokari.

Ya zargesu da nuna halin ko in kula a kan kashe-kashen da ke faruwa a sassan kasar nan. Ya ce 'yan bindiga da mayakan ta'addancin Boko Haram na cin karensu babu babbaka.

A bidiyon mai tsawo, Lance Corporal Martins ya ce shugabannin tsaron Najeriya sun gaza.

Ya kushe shugabannin tsaron Najeriya ballantana Buratai da shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Abayomi Gabriel Olonisakin, a kan yadda ake ci gaba da kashe-kashe.

Ya zargi cewa rundunar sojin ta bada umarnin tsare wasu dakarun wadanda suka bukaci makamai na zamani don yakar Boko Haram da sauran 'yan ta'adda a kasar nan.

Ya tabbatar da cewa akwai yuwuwar a kama shi ko kuma a kashesa saboda wannan bidiyon amma ya ce ya sadaukar da kansa ga kasarsa.

An kama sojan da ya yi wa Buratai da shugabannin tsaro kaca-kaca
An kama sojan da ya yi wa Buratai da shugabannin tsaro kaca-kaca. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Instagram

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta yi wa Gwamna Matawalle kiran gaggawa

A wani labari na daban, sautin fashewar wasu abubuwa masu girzgiza kasa a cikin dajin jihar Zamfara a sa'o'in farko na ranar Talata ya firgita manoma yayin da suke ayyuka a gonakinsu, jaridar Daily Trust ta gano.

Fashe-fashen wanda aka ji a wani daji kusa da yankin Rukudawa da ke da nisan kilomita 7 tsakaninsa da garin Zurmi na karamar hukumar Zurmi, ya matukar tada hankalin jama'a da yawa.

Wani mazaunin yankin mai suna Mustapha Saadu, ya ce wurin karfe 7 na safe ne suka fara jin fashewar abubuwan daga garin Zurmi.

Kowanne sauti kuwa na hade da tsananin kara tare da girgizar kasa wanda ke barazanar yaye kwanon saman gidajen jama'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel