Mamba a majalisah John Abah ya mutu da safiyar ranar Laraba
Majalisar dokokin jihar Kogi ta yi rashin daya daga cikin mambobinta, Honarabul John Abah.
Abah, mamba mai wakiltar mazabar Ibaji a majalisar jihar Kogi ta 8, ya mutu ne a cikin awoyin safiyar ranar Laraba.
Kafin mutuwarsa, marigayin ya na cin zangonsa na biyu a majalisar dokokin jihar Kogi.
Demi Olugbemi, sakataren yada labaran kakakin majalisar jihar Kogi, Mathew Kolawale, shine ya tabbatar da mutuwar Abah a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
DUBA WANNAN: Sanatan APC daga arewa ya amince zai karbi belin Maina
Babu labarin cewa ya sha fama da wata rashin lafiya kafin mutuwarsa, ya mutu ne 'bagatatan', kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng