Yanzu-yanzu: An gano gwamnan Ekiti na cikin masu haddasa rikici cikin APC, ya shigar da Giadom Aso Villa

Yanzu-yanzu: An gano gwamnan Ekiti na cikin masu haddasa rikici cikin APC, ya shigar da Giadom Aso Villa

A ranar Talata, gwamnan jihar Ekiti ya shigar da mataimakin sakataren jam'iyyar All Progressives Congress(APC) Victor Giadom fadar shugaban kasa domin hada shi da shugaba Muhammadu Buhari amma bai samu nasara ba.

The Nation ta samu labarin Fayemi ya shigar da Giadom fadar shugaban kasan ne don mikashi ga Buhari matsayin shugaban uwar jam'iyyar.

Hakazalika an tattaro cewa Fayemi ya kai Giadom ganin Buhari ne domin samun goyon bayansa wajen shirya taron kwamitin zartarwar jam'iyyar.

Amma aka hanasu ganin Buhari duk da dagewar da sukayi.

Kawai sun gana ne da shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, wanda ya ce Buhari ya tashi daga aiki a lokacin.

Fayemi, wanda shine shugaba kungiyar gwamnonin Najeriya na daya daga cikin yan adawar Oshiomole a jam'iyyar APC.

Fayemi ya kai Giadom fadar Aso villa duk da cewa kotu ta tabbatar da sallamar Giadom daga jam'iyyar APC.

Yanzu-yanzu: An gano gwamnan Ekiti na cikin masu haddasa rikici cikin APC, ya shigar da Giadom Aso Villa
Victor Giadom
Asali: UGC

KU KARANTA: Bankin Duniya ta amince da baiwa Najeriya bashin $750m don inganta wutan lantarki

Legit Hausa ta ruwaito muku jiya cewa wata kotun jihar Ribas ta haramtawa mataimakin sakataren uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Victor Giadom ikirarin kansa da kasancewa mamban APC ko shugabanta.

The Nation ta samu rahoton cewa Alkali C. Nwogu ya bada umurnin haka ne a karar da Okechukwu Chidor Ogbonna da Mac-Lords Peterson suka shigar kan jam'iyyar APC na yankin Rivers, mukaddashin jam'iyyar na Rivers Igo Aguma; Victor Giadom da Golden Chioma.

Kotun ta ce tun da kwamitin zartarwar jam'iyyar APC na jihar ta dakatad da Victor Giadom, kada ya sake alakanta kansa da jam'iyyar ko ayyukanta har sai an kammala shari'ar.

Alkalin yace: "An bada umurnin haramtawa mai amsa zargi na uku daga ikirarin kansa matsayin mamba ko jami'in jam'iyyar....ko yin wani abu da ya halasta ga mambobi."

Alkalin ya dage karar zuwa ranar 9 ga Yuli, 2020 domin cigaba da sauraron kara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel