Zaben 2023: Kujerar shugaban kasa ta mutanen Ibo ce – Inji Jim Nwobodo

Zaben 2023: Kujerar shugaban kasa ta mutanen Ibo ce – Inji Jim Nwobodo

Jim Nwobodo wanda ya taba yin gwamna a tsohuwar jihar Anambra a jamhuriyya ta biyu, ya ce a zaben shekarar 2023, mai neman takarar shugaban kasa zai fito ne daga yankin kasar Ibo.

Sanata Jim Nwobodo ya ce shiyyar Kudu maso gabashin Najeriya za su fito da shugaban kasa, ba kowa ba a 2023. Tun yanzu wasu sun fara hangen wanda zai gaji Muhammadu Buhari.

A cewar Jim Nwobodo, fito da shugaban kasa daga yankin na Ibo shi ne adalci da gaskiya da kuma raba dai-dai. Wannan ya sa dattijon ya yi kira ga duk wata jam’iyya ta kai takararta yankin.

Nwobodo ya yi magana ne a ranar Litinin a gidansa da ke garin Enugu, a lokacin da ya ke karbar sarautar gargajiyar 'Eziokwu bu Ndu’ da mai martaba sarkin kasar Amuri ya ba shi.

Tsohon gwamnan ya ce duk wanda ba ya goyon bayan Ibo ya zama shugaban kasa a zabe mai zuwa, ba masoyin Najeriya ba ne, ya ce lokacin ya yi da kabilar za su mulki kasar nan.

KU KARANTA: Yariman Bakura zai nemi kujerar Shugaban kasa a 2023

Zaben 2023: Kujerar shugaban kasa ta mutanen Ibo ce – Inji Jim Nwobodo
Shugaba Buhari tare da su Jim Nwobodo
Asali: UGC

“2023 za ta zama lokacin da mutanen Kudu maso gabas za su fito da shugaban kasa. Don haka ina kiran sauran bangarorin Najeriya su marawa wannan shiri baya domin adalci da gaskiya.”

Sanata Nwobodo ya cigaba da cewa: “Yankin Kudu maso gabas sun cancanci su fito da shugaban kasa na gaba wanda zai gaji Muhammadu Buhari a tafiyar siyasar da ake kai a yanzu.”

Ganin yadda tsarin Najeriya ya ke kai a kan murafu tsakanin Arewa da Kudu da Gabas, Sanata Nwobodo ya ce abin da ya fi dacewa shi ne sauran bangarori su fito su marawa Ibo baya.

A karshe Jim Nwobodo ya godewa mai martaba Amuri, Igwe Charles Nwoye, da ya ba shi wannan sarauta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel