Da duminsa: Bankin Duniya ta amince da baiwa Najeriya bashin $750m don inganta wutan lantarki

Da duminsa: Bankin Duniya ta amince da baiwa Najeriya bashin $750m don inganta wutan lantarki

Bakin Duniya ta amince da baiwa Najeriya bashin $750m (kimanin N30bn) ta kungiyar IDA domin kara inganci da samar da isasshen wutan lantarki a Najeriya, The Cable ta ruwaito.

A takardar da aka saki ranar Talata, bankin ya ce za'a bada bashin ne domin farfado da sashen wutan lantarki ta hanyar ingantashi da tabbatar da gaskiya.

A cewar bankin shirin zai samar da yawan Migawat na wuta 4500 a kowani awa nan da 2022.

A yanzu, Najeriya na fama da kimanin Migawat na wuta 3000 domin rabawa yan Najeriya wuta.

A cewar Diraktan bankin duniya na ofishin Najeriya, Shubham Chaudhuri, ya ce isasshen wutan lantarki zai yi tado da mutane milyan 100 daga cikin bakin talauci a Najeriya.

Da duminsa: Bankin Duniya ta amince da baiwa Najeriya bashin $750m don inganta wutan lantarki
Da duminsa: Bankin Duniya ta amince da baiwa Najeriya bashin $750m don inganta wutan lantarki
Asali: Depositphotos

Yace: "Rashin ingantaccen wutan ya zama cikas da kasuwanci da samar da aikin yi, kuma shi ake bukata wajen fitar da yan Najeriya milyan 100 daga cikin talauci."

"Manufar wannan shiri shine kawo sauyi sashen wutan lantarki da daurashi kan turba na cigaba."

"Wannan na da muhimmanci musamman yanzu da gwamnatin kasar ke bukatar kudade domin taimakawa rayukan mutane cikin halin annobar COVID-19."

A cewar bankin duniya, kashi 47% na mazauna Najeriya basu samun wutan lantarki gaba daya kuma yan kalilan da suke samu na fuskantar daukewa akai-akai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel