Zamfara: Tashin 'abubuwa masu fashewa' a dazuzzuka ya firgita manoma

Zamfara: Tashin 'abubuwa masu fashewa' a dazuzzuka ya firgita manoma

Sautin fashewar wasu abubuwa masu girzgiza kasa a cikin dajin jihar Zamfara a sa'o'in farko na ranar Talata ya firgita manoma yayin da suke ayyuka a gonakinsu, jaridar Daily Trust ta gano.

Faseh-fashen wanda aka ji a wani daji kusa da yankin Rukudawa da ke da nisan kilomita 7 tsakaninsa da garin Zurmi na karamar hukumar Zurmi, ya matukar tada hankalin jama'a da yawa.

Wani mazaunin yankin mai suna Mustapha Saadu, ya ce wurin karfe 7 na safe ne suka fara jin fashewar abubuwan daga garin Zurmi.

Kowanne sauti kuwa na hade da tsananin kara tare da girgizar kasa wanda ke barazanar yaye kwanon saman gidajen jama'a.

"Bayan nan, sai sautin ya dauke babu amon shi.

"Mun shirya mun nufi gonakinmu amma sai muka fara jin shi wurin karfe 9 na safe. Sai muka fara ganin jiragen yaki na kai-kawo a yankin.

"Tuni muka firgice tare da gaggauta komawa gida bayan barin gonakinmu da muka yi.

"Muna zargin jiragen yakin dakarun soji ne ke yi wa sansanin 'yan bindiga ruwan wuta," yace.

Har a lokacin da aka rubuta wannan rahoton, ba a samu jin ta bakin rundunar sojin saman Najeriya da ke Gusau ba.

Zamfara: Tashin 'abubuwa masu fashewa' a dazuzzuka ya firgita manoma
Zamfara: Tashin 'abubuwa masu fashewa' a dazuzzuka ya firgita manoma. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnoni 5 da suka yi kaca-kaca da mataimakansu, suka nakasa su a siyasance

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a ranar Talata ya yi bayanin inda ta kwana ga shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari a kan tsaron jiharsa.

Gwamnan ya ce cibiyoyin tsaro na kokarin ganin sun shawo kan matsalar 'yan bindiga da kuma rikicin jihar Zamfara, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A yayin zantawa da manema labaran gidan gwamnati jim kadan bayan tattaunawar sirrin da suka yi, Matawalle ya ce gwamnati ta tsananta tsaro domin dawo da zaman lafiya a fadin jihar.

Ya ce: "Na samu ganawa da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa a kan al'amuran da suka addabi jihar Zamfara.

"Mun tattauna sosai a kan matsalar tsaron arewacin Najeriya ba wai jihar Zamfara kadai ba.

"Mun samu ganawa da mai bada shawara na musamman a kan tsaron kasa, gwamnonin arewa da kuma sifeta janar din 'yan sandan Najeriya.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ne ya gayyaceni kuma na yi mishi bayanin halin rashin tsaro da jihata take ciki. Mun kuma fahimci inda muka dosa.

"Gwamnatin jihar Zamfara tare da sauran cibiyoyin tsaro na iyakar kokarinsu wajen tabbatar da an shawo kan matsalar rashin tsaro."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel