Rusau: Shugaban kasar Ghana ya kira Buhari, ya nemi afuwar Najeriya

Rusau: Shugaban kasar Ghana ya kira Buhari, ya nemi afuwar Najeriya

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya kira takwaransa na Najeriya, Muhammadu Buhari, a kan rushe wani gini mallakar ofishin jakadancin Najeriya a Accra, babban birnin kasar Ghana.

Yayin hirarsu ta wayar tarho a ranar Talata, Akufo-Addo ya bayyana nadamarsa tare da neman afuwa a kan abinda ya faru har ya fusata gwamnati da 'yan Najeriya.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a daren ranar Talata.

Shugaban kasar Ghana ya bawa shugaba Buhari tabbacin cewa ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike a kan lamarin tare da bashi tabbacin cewa za a hukunta masu hannu a rushe ginin.

A wata majiyar, an bayyana cewa an kama wadanda ake zargin suna da hannu a rushe ginin kuma za a gurfanar dasu a gaban kotu.

Rusau: Shugaban kasar Ghana ya kira Buhari, ya nemi afuwar Najeriya
Sashen ginin ofishin jakadancin Najeriya da aka rushe
Asali: UGC

Wani dan kasuwane ya jagoranci tawagar jami'an tsaro zuwa rushe wani bangare na ginin gidajen ma'aikatan ofishin jakadancin Najeriya bayan ya yi ikirarin cewa an gina wurin a cikin filinsa.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kubutar da leburori 600 da wasu Indiyawa suka kulle a wani kamfani a Kano

Kafin rushe ginin a ranar Juma'a, mutumin ya ziyarci rukunin gidajen domin gabatar da wasu takardu a matsayin shaidar cewa shine ya mallaki wurin.

Ofishin jakadancin Najeriya ya sanar da gidan talabijin na 'Channels' cewa bai dakatar da mutumin ba saboda sun aikawa gwamnatin kasar Ghana korafi a rubuce amma ba ta mayar da martani ba.

Manyan shugabannin Najeriya da suka hada da ministan harkokin kasashen waje da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, sun yi tir da rushe ginin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel