COVID-19: An gano wata barazanar lafiya da wadanda suka warke daga korona ke fuskanta

COVID-19: An gano wata barazanar lafiya da wadanda suka warke daga korona ke fuskanta

Likitoci sun gargadi dubban wadanda suka warke daga cutar COVID-19 cewa akwai yiwuwar su kamu da ciwon huhu don haka akwai bukatar su sake komawa asibiti a duba su nan gaba.

Kwararru a fanin kiwon lafiya da suka yi hira da BBC sun ce akwai yiwuwar wadanda suka warke daga korona su samu rauni a huhunsu mai suna 'pulmonary fibrosis.'

Alamun na pulmonary fibrosis da a halin yanzu ba shi da magani sun hada da rashin yin numfashi, tari da yawan kasala.

Anthony McHugh, wani tsohon direban tasi ya rika fama da wadannan alamomin bayan an kwantar da shi a asibiti a ranar 6 ga watan Maris sakamakon alamomin korona da ya ke da shi.

Daga baya an sallame shi a cikin watan Afrilu bayan an masa magani amma watanni biyu bayan sallamar, McHugh ya cigaba fama da matsalar rashin yin numfashi kamar yadda ya kamata.

COVID-19: An gano wata barazanar lafiya da wadanda suka warke daga korona ke fuskanta
COVID-19: An gano wata barazanar lafiya da wadanda suka warke daga korona ke fuskanta. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kalli bidiyon yadda sojoji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a matattaransu da ke Bula Korege

"Idan nayi kananan ayyuka kamar hawa bene ko bawa shuka ruwa. Yana zama dole sai na tsugunna in huta," kamar yadda ya shaidawa wata kafar watsa labarai.

Hoton kirgin McHugh da aka dauka a asibiti watanni shida bayan sallamarsa ya nuna wasu siraren fararen layyuka da ke nuna alamun pulmonary fibrosis.

Za a sake daukan hoton kirginsa bayan watanni 12 a duba idan raunin da ke huhun na cigaba da tabarbarewa.

Sam Hare, mamba a kwamitin kungiyar kwararru masu nazarin ciwon kirji (BSTI) yace wannan lamari ne da ya dace a mayar da hankali a kansa.

Hare, ya kara da cewa a halin yanzu ba a gudanar da isashen bincike ba da za a iya gane illar da COVID-19 ke yi wa huhu.

Ya ce, "A halin yanzu ba za mu iya cewa ga tabbacin abinda ke faruwa ba."

"Yadda aka saba shine idan mutum ya kamu da kwayar cuta ya warke, bayan watanni shida ya kamata huhunsa ya koma yadda ya ke. Amma a wannan karon ba haka ya ke ba shi yasa muka damu."

BBC ta ruwaito cewa wani darasi da aka gudanar a China da aka wallafa a watan Maris ya nuna cewa 66 cikin majinyata 70 suna da rauni a huhunsu bayan an sallamesu daga asibiti.

Wasu likitoci a Ingila da suka goyi bayan wannan nazarin sun ce suma sun lura cewa kashi 30 cikin masu korona da suka warke suna nuna alamun ciwon huhu.

Hare ya ce an samu irin wannan matsalar a mutanen da suka kamu da kwayar cutar Sars da Mers - wadanda suka nau'ika ne na coronavirus.

Gisli Jenkins, Farfesa a Cibiyar Bincik ta Ingila, NHS, ta ce akwai bukatar ayi nazarin matsalar da nufin gano yadda za a magance shi.

Saboda damuwar da likitoci keyi a kan lamarin, NHS ta sanar da cewa za ta bude cibiyoyin kwararru da za su rika kulawa da wadanda suka warke daga coronavirus.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel