Sarki a Najeriya ya shiga jerin manyan sarakuna 5 a nahiyar Afrika

Sarki a Najeriya ya shiga jerin manyan sarakuna 5 a nahiyar Afrika

- Sarki Mohammed VI na Morocco shine sarki mafi arziki a nahiyar Afirka, kudinsa ya kai $ biliyan 2

- Sarakuna na biyu da na uku sune Sarki Fredrick Obateru Akinruntan da marigayi Sarki Olubuse II da $300m da $75m

- Akwai sarki daga Najeriya cikin jerin sarakuna biyar da suka fi arziki kamar yadda Wikipedia ta wallafa

Shafin tattara bayanai na Wikipedia ta lissafa sarakunan nahiyar Afirka da suka fi kudi. Shafin ya ruwaito cewa an wallafa sunayen ne a mujjalar Forbes a shekarar 2014.

Amma shafin ta yi bita kan bayanan da ta wallafa a kan sarakunan a ranar Alhamis 28 ga watan Mayun 2020.

Sarki Mohammed VI na kasar Morocco ne sarkin da ya fi sauran kudi a jerin sunayen sarakunan da Dallar Amurka biliyan 2.

Mai biye masa shine Sarki Fredrick Obateru Akinruntan na masarautun Olugbo da Ugbo a Najeriya da kudi Dalla miliyan 300.

Ga jerin sunayen sarakunan da jumullar kudin da suka mallaka:

1. Sarki Mohammed VI na Morocco - $2bn (Morocco)

2. Sarki Fredrick Obateru Akinruntan - $300m (Najeriya)

3. Sarki Olubuse II, marigayi Ooni na Ife - $75m (Najeriya)

4. Sarki Mswati III, Ngwenyama na Eswatini - $50m (Estwatini)

5. Sarki Osei Tutu II, Asantehene na Ashanti - $10m (Ghana)

Attajiran sarakunan nahiyar Afirka
Attajiran sarakunan nahiyar Afirka. Hotuna daga Moroccan Times/GhanaWeb/DailyPost
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kalli bidiyon yadda sojoji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a matattaransu da ke Bula Korege

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa Aliko Dangote shine mutum da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka inda ya mallaki Dalla biliyan 9.5 sai mai biye masa Nicky Oppenheimer daga kasar Afrika ta Kudiu da Dalla biliyan 7.5.

Wani dan Najeriya da ke cikin jerin attajiran na Afirka shine Mike Adenuga da Dalla biliyan 5.8 (N2,244,600,000,000).

Rabiu shine na uku a Najeriya da Dalla biliyan 3.2 (N1,238,400,000,000).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel