Yadda aka bindige mutum hudu har lahira a Abuja

Yadda aka bindige mutum hudu har lahira a Abuja

Wasu da ake zargin yan bindiga ne a yammacin ranar Lahadi sun harbe mutum hudu har lahira a kauyen Yanbabu da ke hanyar Kwaita – Kwakwu da ke karamar hukumar Kwali ta Abuja.

Wani mazaunin garin mai suna Ishaku ya ce lamarin ya faru ne yayin da wani direban babban mota da karen motarsa suka bar kasuwan Kwali zuwa kauyen Kwaku.

Ya ce 'yan bindigan dauke da makamansu suka fito kwatsam daga cikin daji suka bude wa motar wuta inda suka kashe karen motar nan take.

Yadda aka bindige mutum hudu har lahira a Abuja
Yadda aka bindige mutum hudu har lahira a Abuja. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

A cewarsa sun tisa keyar sauran mutum ukun zuwa cikin daji a kan babur.

"Yan banga sun bi sahun masu garkuwa da mutanen da niyyar ceto wadanda aka sace sai dai abin bakin ciki sun riga sun kashe wadanda suke sace kuma sun tsere," in ji shi.

Ya ce 'yan bangan sun kwaso gawarwarkin mutanen uku sun dawo da su cikin gari domin 'yan uwansu su musu jana'iza.

DUBA WANNAN: Kalli bidiyon yadda sojoji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a matattaransu da ke Bula Korege

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Abuja, DSP Anjuguri Manza, ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwar da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin a Abuja.

Ya ce rundunar ta fara bincike a kan lamarin domin ceto wasu mutane da masu garkuwa da mutanen suka sace a garin.

Har wa yau, ya bukaci mutanen kauyen da sauran al'umma su kwantar da hankulansu su cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba su bawa rundunar goyon baya domin ta inganta tsaro a garin da sauran sassan Abuja.

A wani labarin, kun ji cewa gwamnonin jihohin arewa sun yanke hukuncin saka mafarauta da 'yan banga domin yakar matsalar 'yan bindiga da duk wani nau'in rashin tsaro da ke yankin.

Wannan ya biyo bayan yawaitar kashe-kashe a jihohin Katsina, Zamfara da sauran jihohin yankin, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Kungiyar gwamnonin arewa, wadanda suka yi taro ta yanar gizo don sake duba yanayin tsaron yankin, sun samu shugabancin Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong.

Gwamnan ya nuna damuwarsa da yadda rashin tsaro ke ci gaba da ta'azzara a yankin wanda ya kai ga rashin rayuka da kadarori.

Gwamnonin sun yanke hukuncin kafa kwamitin da zai dinga lura da tsaron yankin wanda zai samu shugabancin Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi. Kwamitin ya kunshi gwamnan jihar Zamfara da na jihar Gombe a matsayin mambobi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel