'Yan daba sun kai wa magoya bayan gwamnan APC hari, sun raunata wasu

'Yan daba sun kai wa magoya bayan gwamnan APC hari, sun raunata wasu

Wasu matasa da ake zargin 'yan bangar siyasa ne sun kai hari a yayin da wata kungiyar magoya bayan gwamnan jihar Ondo, Gwamna Rotimi Akeredolu, ke taro a garinsu na Owo da ke karamar hukumar Owo ta jihar a yammacin ranar Lahadi.

An tabbatar da cewa 'yan daban sun raunata da yawa daga cikin mambobin APC da suka halarci taron da aka yi a yankin Igboroko da ke garin, jaridar The Punch ta ruwaito.

Sun ragargaza motocin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu a karo na biyu.

Kamar yadda ganau ba jiyau ba suka tabbatar, 'yan dabar sun isa yankin ne yayin da ake taron. Sun fara harbe-harbe babu kakkautawa don ankarar da jama'ar wurin zuwansu.

Da yawa daga cikin masu goyon bayan gwamnan sun samu harbin harsasan da aka dinga ruwansu a wurin, jaridar The Punch ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Olayemi Olamide, ya zargi cewa daukar nauyin harin aka yi. Ya dora zargin a kan daya daga cikin abokan hamayyar gwamnan wanda ke neman kujerar gwamnan jihar na APC.

'Yan daba sun kai wa magoya bayan gwamnan APC hari, sun raunata wasu
'Yan daba sun kai wa magoya bayan gwamnan APC hari, sun raunata wasu. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnonin arewa za su aika da mafarauta da 'yan banga su yaƙi 'yan bindiga

Ya ce, "Muna tsaka da taron da muka bayyana goyon bayanmu a kan tazarcen Gwamna Akeredolu ne 'yan daba dauke da miyagun makamai suka isa dakin taron a cike da motoci uku.

"'Yan daban sun dinga harbe-harbe a iska sannan sun lalata motocin kamfen din da muka ajiye a gefen titi. Jama'a sun dinga gudun ceton rai yayin da 'yan daban suka dinga harbi na tsawon sa'a daya.

“Da yawa daga cikin jama'armu sun samu raunika sakamakon harbin bindiga."

A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Tee-Leo Ikoro, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma ya ce babu wanda ya rasa ransa kuma rundunar bata kama ko mutum daya ba da ke da hannu a cikin aika-aikar.

"Muna da tabbacin aukuwar lamarin don jami'anmu sun ziyarci wurin da abun ya faru.

'Wasu jama'a da ake zargin 'yan bangar siyasa ne suka dinga harbi babu kakkautawa, amma basu kashe kowa ba sannan bamu kama ko mutum daya ba.

"Mun fara bincike a kan al'amarin," Ikoro yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel