Edo 2020: Dan takarar APC, Ize-Iyamu ya bukaci Obaseki ya dawo APC

Edo 2020: Dan takarar APC, Ize-Iyamu ya bukaci Obaseki ya dawo APC

Fasto Osagie Ize-Iyamu, dan takarar jam'iyyar APC a jihar Edo, ya bukaci Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo da ya dawo jam'iyyar APC.

Obaseki ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP bayan hana shi takara da jam'iyyar ta yi bayan ta ce bai cancanta tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar ba da za a yi a watan Satumba.

Ize-Iyamu, wanda ya yi takarar kujerar gwamnan jihar a 2016 karkashin jam'iyyar PDP ya sha mugun kaye a hannun Obaseki a wancan lokacin, jaridar The Cable ta ruwaito.

Sakamakon rashin jituwar da ke tsakanin Obaseki da Adams Oshiomhole, Ize-Iyamu ya samu karbar tikitin takara a karkashin jam'iyyar APC bayan ya bar PDP ya koma APC.

An gano cewa Adams Oshiomhole na goyon bayan Fasto Osagie Ize-Iyamu.

Bayan bayyana shi a matsayin dan takara karkashin jam'iyyar APC a ranar Litinin, Ize-Iyamu ya ce yana son yi aiki da Obaseki matukar zai dawo 'asalin jam'iyyarsa'.

"Bayan kammala wannan gasar, zan iya cewa jam'iyyar na komawa daidai. Ina jinjina ga Gwamna Obaseki kuma ina rokonsa da ya dawo jam'iyyar APC," yace.

Edo 2020: Dan takarar APC, Ize-Iyamu ya bukaci Obaseki ya dawo APC
Edo 2020: Dan takarar APC, Ize-Iyamu ya bukaci Obaseki ya dawo APC. Hot daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ku zage damtse, ko mu saita muku hanya - Lawan ga Shugabannin tsaro

"A kowacce jam'iyya, ana samun rashin jituwa amma abinda ban so ba shine yadda wannan rashin jituwar ta sa ya bar jam'iyyyar. Na taba yin kuskure. Zan ji dadi idan ya dawo kuma babu shakka zan yi aiki tare da shi.

"Mun nuna misali a yau. Muna tabbatar da cewa za mu bi doka. Watanni kalilan da suka rage mana na yakin neman zabe, mu yi kokarin kiyaye doka.

"A madadina da na jam'iyyarmu, na dauka alkawarin cewa za mu tabbatar da zaman lafiya tare da mutunta doka.

"A gaskiya ina matukar farin ciki kuma ina jin dadin yadda na samu goyon baya daga kananan hukumomi 18 na jihar nan.

"Na yi farin ciki yadda ba a samu rikici ba. An yi zaben cike da kiyaye dokar gwamnatin jihar nan ta dakile yaduwar annobar korona."

Ize-Iyamu ya ce idan ya yi nasarar lashe zaben a watan Satumba, zai yi aiki tare da kowa don ganin ci gaban jihar.

Ya mika godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Oshiomhole da dukkan jami'an tsaro a kan goyon bayan da suka bada yayin zaben fidda gwanin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: