Watakila mu fara daukar mutanen da su ka mutu a daruruwa nan da makonni uku - Boss Mustapha

Watakila mu fara daukar mutanen da su ka mutu a daruruwa nan da makonni uku - Boss Mustapha

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da annobar COVID-19 a Najeriya, Mista Boss Mustapha ya gargadi mutane game da yaduwar wannan mummunan cutar a kasa.

Boss Mustapha ya ce za a fara daukar mutane a daruruwansu nan da makonni uku, a dalilin yaduwar da cutar ta ke yi. Hakan na zuwa ne bayan an samu mutane kusan 20, 000 da su ka kamu a Najeriya.

A ranar Asabar an gano sababbin mutane 661 da cutar COVID-19 ta harba, daga ciki akwai mutane 230 a Legas, 127 a Ribas, 83 a Delta, 60 a babban birnin tarayya da 25 da 2 a Kaduna da jihar Kano.

Mustapha a madadin kwamitin shugaban kasa na PTF ya bayyana cewa yawan gwajin da ake yi wa mutane yanzu ne ya sa alkaluman su ka tashi, ake samun labarin karin masu dauke da Coronavirus.

Shugaban kwamitin yaki da annobar ya ce Najeriya ba ta kai ga shiga wani zagaye na barkewar cutar a halin yanzu ba, wanda a cewarsa babu yadda za a iya hana hakan faruwa nan gaba.

KU KARANTA: COVID-19 za ta cigaba da ta’adin kashe Bayin Allah – PTF

Watakila mu fara daukar mutane a daruruwa nan da makonni uku - Boss Mustapha
SGF Boss Mustapha
Asali: UGC

SGF ya koka da halin wasu ‘Yan Najeriya na nuna ko-in-kula a lokacin da cutar ta ke cigaba da kara yaduwa, ya ce idan aka fara samun yawan masu mutuwa, mutane za su shiga cikin dar-dar.

Sakataren gwamnatin na kasar ya yi bayani cewa yawan gwajin da ake yi zai yi tasari a kan adadin wadanda za su mutu.

“Alkaluman da ku ke gani ya na da alaka ne da karfin gwajin kasar. Mun kara yawan wadanda ake yi wa gwaji. Daga dakunan gwaji biyu, yanzu mu na da fiye da 30.” inji Mustapha.

Mista Mustapha ya kara da cewa: “Saboda haka alkaluman da ku ke gani yanzu, a karshe zai kai ga samun karuwar adadin wadanda cutar za ta kashe a nan da makonni uku, wannan zai fara nunawa.”

“Za a shiga cikin rudani, za mu rude, abin takaici har yanzu mu na fama da guguwar farko na annobar ne, alkaluman ba za su yi kasa ba.” Mustapha ya ce don haka dole a bi dokoki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng