Dogarin Aisha Buhari ya dawo bakin aiki bayan harbe-harben fadar Shugaban kasa

Dogarin Aisha Buhari ya dawo bakin aiki bayan harbe-harben fadar Shugaban kasa

Bayan bincike, an wanke ADC watau Dogarin mai dakin shugaban Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, kuma har ya koma bakin aikinsa.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa wani kwamiti ya binciki ADC Usman Shugaba wanda jami’in ‘dan sanda ne, an kuma samu tabbacin cewa bai da hannu wajen aikata wani laifi.

A dalilin haka aka dawo da Usman Shugaba bakin aiki na gadin uwargidar shugaban kasa. Haka zalika sauran mukarraban jami’an tsaron da ke tare da Aisha Buhari sun koma aiki.

An samu takaddama a fadar shugaban kasar ne a dalilin sabanin da aka samu tsakanin Hajiya Buhari da wani daga cikin hadiman mai gidanta, shugaba kasa Muhammadu Buhari.

Wannan sabani tsakanin ‘yan gidan shugaban kasar ya jawo harbi a fadar Aso Rock, hakan ya yi sanadiyyar tsare Dogarin Aisha Buhari da wasu daga cikin tawagar ‘yan sandan na ta.

Tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya yi jawabi, ya bukaci a binciki lamarin.

KU KARANTA: An ji harbin bindiga kamar ana neman yin juyin-mulki a Aso Villa

Dogarin Aisha Buhari ya dawo bakin aiki bayan harbe-harben fadar Shugaban kasa
Mai dakin Shugaban kasa Aisha Buhari Hoto: Pulse
Asali: UGC

A ranar Asabar, 20 ga watan Yuni, kwamitin da aka kafa domin ya yi bincike, ya wanke ADC.

Wata majiya mai karfi ta shaidawa jaridar cewa: “Uwargidar shugaban kasar ta yi kokarin ganin an dawo mata da duk ma’aikatanta, bayan kwamitin ya gano cewa ADC din bai yi harbi ba.”

“An gano cewa ADC din ba ya cikin fadar shugaban kasar, kuma ba ya rike da bindiga a lokacin da abin ya faru.” Inji majiyar.

“Kwamitin binciken ya kuma gano cewa babu wasu ‘yan sanda da ke rike da makamai. An samu sabani ne kurum a game da bin sharudan kare kai daga kamuwa da cutar COVID-19.”

Abin da ya faru shi ne an samu wanda ya yi tafiya zuwa Legas yayin da ake fama da COVID-19, don haka Buhari ta bukaci lallai ya killace kansa, wannan ya jawo sabani a tsakaninsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel