Rundunar soji ta yi wa dakarunta 342 ritaya

Rundunar soji ta yi wa dakarunta 342 ritaya

A ranar Juma'a ne rundunar sojin Najeriya ta yi wa sojoji 342 ritaya daga aiki bayan wadata su da sana'o'in dogaro da kai.

Wadanda aka yi wa ritayar sun hada da sojin kasa 243, na ruwa 100 sai na sama 16 bayan watanni shida da suka kwashe a sansanin Nigerain Armed Forces Resettlement Centre (NAFRC) da ke Oshodi a jihar Legas.

An koyar da su sana'o'i wadanda za su iya yi don dogaro da kai bayan barin aiki, jaridar The Nation ta ruwaito.

A yayin jawabi ga sojin masu murabus, kwamandan NAFRC, Air Vice Marshal Kingley ya ce sune kashi na farko da suka yi murabus a wannan shekarar.

Ya kara da cewa kashi na biyu da za su yi murabus a wannan shekarar sun kai 100.

Ya jinjinawa masu ritayar ta yadda suka kwashe shekaru 35 na rayuwarsu suna bautawa kasa da karfinsu tare da lafiyarsu.

"A yayin da muke yaye ku, kuna barin rayuwar soja inda za su koma tsoffin ma'aikata masu bada gudumawarsu ga Najeriya," AVM Lar ya sanar da masu murabus.

Kamar yadda ya sanar, mutum 359 ne aka tsara za su halarci horarwar kafin yin murabus amma wasu daga ciki sun koma bakin aikinsu saboda wasu dalilai.

Daya daga cikinsu kuwa mai mukamin Master Warrant Officer, Garba Mohammed ya rasu a ranar 5 ga watan Yuni.

Rundunar soji ta yi wa dakarunta 342 ritaya
Rundunar soji ta yi wa dakarunta 342 ritaya. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kalli bidiyon yadda sojoji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a matattaransu da ke Bula Korege

"A lokacin da suka taru a watan Janairu, tsoffin sojojin sun kai 365. Wasu sun koma bakin aikinsu saboda wasu dalilai amma an fara horarwar da 343. Dukkansu sun kammala amm\ma mutum daya ya rasu.

"A halin yanzu, mun yaye 342 duk da mun yi taka-tsan-tsan da matakan kiyaye yaduwar COVID-19. Ba mu iya jere 342 duka ba amma 65 daga ciki sun samu halartar bikin.

"Kamar yadda nake fada a kodayaushe, ba za mu iya tsame ci gaba ba daga tsaro. Horarwar da suka samu ce za ta sa su kafa kasuwancin da ya dace tare da yakar rashin aikin yi. Aikin yi na rage al'amuran ta'addanci.

“A don haka hedkwatar tsaro ta amince da gurbi 100 na 'yan sanda da saura cibiyoyin tsaro," yace.

AVM Lar ya ce dokar hana walwala sakamakon COVID-19 bata shafi zirga-zirgar da suka yi ba yayin horarwar don sun aiwatar ne kafin a hana yawp.

Ya kara da bayanin cewa dukkan abinda ya kamata su sani sun sansu a cikin NAFRC.

Duk da annobar korona, kwamandan ya kwatanta masu murabus din da masu sa'a don tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawo kan matsalolin da za su iya fuskanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
NDA
Online view pixel