Gwamnatin tarayya ta sallami matasan N-Power 500,000

Gwamnatin tarayya ta sallami matasan N-Power 500,000

Ministar walwala da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa za'a sallami matasan N-Power da aka dauka a shekarar 2016 wannan watan na Yuni, 2020.

Hakazalika za'a sallami wadanda aka dauka a 2018 a watan Yuli, 2020.

Shirin N-Power ya dauki matasa 500,000; karon farko an debi mutane 200,000 a Satumba 2016, sannan 300,000 a watan Agustan, 2018.

A lokacin da aka daukesu aiki, an bayyana musu cewa watanni 24 za suyi amma matasa 200,000 farko da aka dauka sun kwashe sama da 40,000.

A wani jawabi, Hajiya Sadiya Farouq ta ce gwamnatin tarayya ta fara shirin mayar da su wani shirin aikin hannu.

Gwamnatin tarayya ta sallami matasan N-Power 500,000
Gwamnatin tarayya ta sallami matasan N-Power 500,000
Asali: UGC

KU KARANTA: Sabbin mutane 667 sun harbu da cutar Korona a Najeriya

Tace: "Mun kaddamar da mayar da matasan diban farko da na biyu cikin wasu shirye-shiryen aikin hannu da gwamnati ta shirya tare da hadin kan wasu kamfanoni masu zaman kansu domin daukan matasan aiki.."

"Gwamnatin tarayya za ta cigaba da fadada shirin (N-Power) kuma yanzu zamu fara daukan sabbin matasa."

"Saboda haka, ma'aikatar na sanar da cewa yan diban farko zasu tafi a ranar 30 ga Yuni, 2020 yayinda diba na biyu zasu tafi 31 ga Yuli, 2020."

Ma'aikatar ta ce za'a fara sabon dauka ne daga ranar 26 ga Yuli, 2020.

Za'a bude shafin yanar gizon rijista daga ranar 26 ga Yuni, 2020 domin masu bukata su nema.

N-Power shiri ne da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samar a shekarar 2016 karkashin ofishin jin dadin al'umma.

An samar da shirin ne domin rage yawan matasa marasa aikin yi a Najeriya da kuma rage talauci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel