Mijina ya biya N580,000 sadakina, ya yi alkawarin ba zai tallafi dangina ba - Budurwa ta koka

Mijina ya biya N580,000 sadakina, ya yi alkawarin ba zai tallafi dangina ba - Budurwa ta koka

Wata budurwa 'yar Najeriya ta bayyana yadda mijinta ya ki taimakon 'yan uwanta bayan ya biya sadakinta har kusan N600,000, jaridar The Nation Community ta wallafa.

A wani labari da wata ma'abociyar amfani da kafar sada zumuntar zamani na Twitter mai suna @SmartAtuad ta wallafa, budurwar ta bayyana yadda mijinta ke samun albashin N70,000 duk wata.

Amma kuma a hakan ya dage wajen tara sadakinta na N580,000 da aka yanke masa a gidansu.

Ta bayyana cewa wannan makuden kudin da mijinta ya kashe ne yasa ya dauka alkawarin cewa ba zai kara tallafawa 'yan uwanta ba.

Ya jaddada cewa sirikansa sun karba duk abinda za su ci daga wurinsa.

Aurensu na cikin garari tun bayan da kanin matarsa ya je neman aure amma sai aka bukaci N400,000.

Babu sake wani tunani, mahaifin matarsa ya mika masa bukatar tallafin N120,000 don gudumawar bikin duk da ya san N70,000 yake karba duk wata.

A fusace da bukatar sirikinsa, mijin ya sanar da matarsa cewa ta tuna da rantsuwar da ya dauka na cewa ba zai taba taimakawa 'yan uwanta ba tun bayan da suka zabga mishi sadaki.

A fusace da wannan hukuncin na mijinta, matar ta kira sa da mara kirki.

Saurayina ya biya N580,000 sadakina, ya yi alkawarin ba zai tallafi dangina ba - Budurwa ta koka
Saurayina ya biya N580,000 sadakina, ya yi alkawarin ba zai tallafi dangina ba - Budurwa ta koka. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Kotu ta tabbatar da Giadom a matsayin shugaban APC na kasa

A wani labari na daban, dalibar jami'ar tarayya da ke Oye Ekiti a jihar Ekiti mai suna Faderera Oloyede ta rasu a dakin saurayinta mai suna Ayo Maliki.

Budurwar ta rasu a ranar Talata, 16 ga watan Yunin 2020. Faderera daliba ce da ke aji uku inda take karantar lissafi.

Ta ziyarci saurayinta da ke yankin Koko na Iree a jihar Osun tare da wata kawarta mai suna Kemisola Adewusi.

Kemisola Adewusi daliba ce a jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Kamar yadda wata majiya ta sanar, Maliki ya dafa wa bakinsa shinkafa amma yayin da Oloyede ke ci sai ta fara korafin ciwon ciki.

Babu dadewa ta fara amai. A take kuwa ta ce ga garinku duk da yunkurin ceto rayuwarta da Maliki tare da sauran suka yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel