Edo 2020: Dalilin da yasa zan yi takara karkashin PDP - Obaseki

Edo 2020: Dalilin da yasa zan yi takara karkashin PDP - Obaseki

Gwamnan jihar Oyo, Godwin Obaseki ya sanar da magoya bayansa cewa zai yi takarar kujerar gwamna a 2020 karkashin jam'iyyar PDP.

Obaseki, wanda ya kwatanta hana shi tsayawa takara da jam'iyyar APC tayi da rashin adalci, ya ce komawa jam'iyyar PDP tseratar da shugabanci na gari ne a jihar.

Gwamnan ya kara da cewa PDP ta nuna yuwuwar bashi damar kawo ci gaba mai dorewa a jihar.

Ya sanar da hakan ne jim kadan bayan komawarsa jam'iyyar PDP a ranar Juma'a.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Obaseki ya ziyarci gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da wasu gwamnonin jam'iyyar PDP tun bayan da aka hana shi tsayawa takara a karkashin jam'iyyar APC.

A tsammanin sauya shekar Obaseki, jam'iyyar PDP ta dage zaben fidda gwaninta daga ranar 19 da 20 ga watan Yuni zuwa ranar 23 ga watan Yunin.

Amma kuma, a lokacin fitar da rahoton nan, babu tabbacin cewa Obaseki ne zai bayyana dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar PDP.

Hakazalika, babu tabbacin cewa Obaseki zai fito takara tare da Philip Shaibu a matsayin mataimakinsa.

Edo 2020: Dalilin da yasa zan yi takara karkashin PDP - Obaseki
Edo 2020: Dalilin da yasa zan yi takara karkashin PDP - Obaseki. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mahaifin mai neman takarar gwamna a Edo a APC

Yayin sanar da sauya shekar, Obaseki ya bukaci magoya bayansa a jihar da Najeriya da su koma jam'iyyar PDP.

"Na koma jam'iyyar PDP a Najeriya don tabbatar cikar burina na komawa kujerar gwamnan jihar Edo.

"Kamar yadda kuka sanni, na kasance mai fatan tabbatar da shugabanci nagari da ci gaba mai dawwama a jiharmu ta gado," Obaseki yace.

Sauya shekarsa ya zo ne bayan kwanaki kadan da kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar APC ya aminta da hukuncin kwamitin tantancewar 'yan takara na jihar a kan hana shi fitowa takara saboda wasu dalilai.

A ranar Talata, 16 ga watan Yunin 2020 gwamnan ya bar jam'iyyar APC tare da mataimakinsa Philip Shaibu, jaridar The Punch ta ruwaito.

Kwamitin gudanar da ayyukan wanda ya samu shugabancin Adams Oshiomhole, ta sanar da hana gwamnan takara a ranar 13 ga watan Yunin 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel