Da duminsa: Bayan barazanar sallamarsu, FG ta saki N4.5bn don biyan Likitoci masu yajin aiki
Gwamnatin tarayya ta saki kudi biyan hudu da rabi (N4.5bn) ga manyan asibitocin tarayya 31 dake fadin kasar nan, Channels TV ta rahoto.
Ta bayyana cewa an saki wannan kudin ne matsayin alawus na Likitoci na watan Afrilu da Mayu.
Ministan kwadago a samar da aikin yi, Chris Ngige, ya bayyana hakan ga manema labaran fadar shugaban kasa ranar Juma'a a Abuja, birnin tarayya.
Ministan ya yi jawabin ne bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya koma PDP
A jiya mun kawo muku rahoton cewa kungiyar Likitocin Najeriya ta siffanta barazanar gwamnatin tarayya na sallamarsu daga aiki ko kin biyansu albashi idan basu koma bakin aiki ba a matsayin wasan yara.
Shugaban kungiyar, Aliyu Sokomba, ya bayyana cewa "barkwanci kawai gwamnati keyi" kuma ko kadan hakan ba zai baiwa Likitoci tsoro ba.
Hakazalika ya lashi takobin cewa za su cigaba da yajin aikinsu har sai an biyasu dukkan bukatunsu.
A ranar Talata, gwamnatin tarayya ta yi barazanar sallamar likitocinta daga aiki muddin ba su yi watsi da maganar zuwa yajin-aiki, su ka koma asibitoci domin su cigaba da kula da marasa lafiya ba.
Gwamnatin Najeriya ta umurci likitocin su koma aiki a ranar Laraba, inda ta ce za ayi bincike kuma a hukunta duk wanda aka samu bai hallara a asibiti ba.
Wannan barazana ta fito ne daga bakin ministan harkar lafiya na kasa, Osagie Ehanire, bayan an gaza samun matsaya a zaman tattaunawar da su ka yi da kungiyar manyan likitocin.
Kungiyar NARD likitoci mataki na biyu a Najeriya sun shiga yajin aiki ne a ranar Litinin. Har yanzu dai ministan harkar kiwon lafiyan ya gaza shawo kan likitocin kasar.
A zaman da aka yi ranar Talata wanda aka fara da kimanin karfe 1:00, an tashi baram-baram babu matsaya tsakanin bangarorin inda shugaban NARD, Aliyu Socumba, ya fice a fusace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng