Covid-19: MURIC ta ja kunne a kan bude makarantu da wuraren bauta

Covid-19: MURIC ta ja kunne a kan bude makarantu da wuraren bauta

Kungiyar rajin kare hakkkin Musulmi ta yi jan kunne a kan batun bude makarantu da wuraren bauta.

Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya jinjinawa gwamnatin tarayya da jihohi da suka dakatar da bude makarantu har zuwa wani lokaci tare da dakatar da bude wuraren bauta a jihar Legas.

Akintola ya ce: "Muna tare da gwamnatin tarayya a kan bukatar tsagaita bude makarantu. Har yanzu akwai hatsari babba kuma ba a gano abinda zai faru nan gaba ba.

"Beijing ta bude makarantu amma bayan makonni kadan suka bada umarnin kara rufe makarantun saboda barkewar annobar.

Covid-19: MURIC ta ja kunne a kan bude makarantu da wuraren bauta
Covid-19: MURIC ta ja kunne a kan bude makarantu da wuraren bauta Hoto: Punch
Asali: Facebook

"Sake rufe makarantun na da babbar illa a kan daliban da iyayensu. Za ta iya nuna rashin hadin kan jami'an tsaro."

A saboda haka ne ya bukaci gwamnati da kada ta tafka kuskuren irin wanda Beijing tayi.

"Saboda haka, mun goyi bayan dakatar da bude wuraren bauta a jihar Legas kamar yadda gwamnatin jihar Legas ta yanke.

"Adadin masu cutar yayi yawa da za a bude wuraren bauta. A ranar Laraba, mutum 7,461 ne a jihar Legas aka tabbatar suna dauke da cutar. Wannan na nuna kashi 44 na yawan masu cutar a Najeriya.

"Wannan babban abun tashin hankali ne idan aka danganta jihar da Abia, Ebonyi, Taraba da Binuwai inda babu wanda ya mutu.

"Gaskiya jihar Legas ta dauki matakin da ya dace ta yadda ta dakatar da bude majami'u da masallatai. Ko kasar Saudiyya ta rufe masallatai bayan budesu da tayi. A lura cewa Legas na da mutum miliyan 17.5."

Akintola ya yi kira ga mazauna jihar Legas da su dauka hakuri tare da juriya.

KU KARANTA KUMA: Tsaro: Gwamnonin arewa sun yi taro, sun fitar da sabbin tsare-tsare

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a ranar Laraba ya ja kunnen cewa akwai yuwuwar ya sake saka dokar hana walwala ga jama'ar jihar matukar aka ci gaba da yin watsi da dokokin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Ya yi karin bayani da cewa, "idan yawan masu kamuwa da cutar ya sha karfin cibiyoyin lafiyarmu da ma'aikatanmu, za mu sake rufe jihar."

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin kaddamar da abun hawa na gwaji da USAID ta bai wa jihar.

Ya ce ya dage dokar hana walwalar ne saboda yana da tabbacin jihar na da kayan gwaji da dakunan gwaji isassu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel