Harbi a Aso Rock: An sauya wa dogarai 20 na Buhari wurin aiki

Harbi a Aso Rock: An sauya wa dogarai 20 na Buhari wurin aiki

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin sauya wa dogaransa 20 wurin aiki sakamakon harbin da aka yi a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

An janye jami'an hukumar tsaro ta fararen kaya da jam'ian tsaro na sirri daga fadar shugaban kasar sakamakon kasa shawo kan al'amarin da suka yi, wanda ya kai ga harbi a fadar.

Ana tsammanin za a maye gurbinsu da sabbi babu dadewa.

Harbin ya kawo firgici don an yi tsammanin shugaban kasar na cikin hatsari, amma daga bisani Buhari ya bada umarnin bincike a kan al'amarin.

An yi harbin a fadar shugaban kasa bayan uwargidansa tare da 'ya'yansa uku - Zahra, Halima da Yusuf - tare da wasu jami'an tsaronsu da suka samu jagorancin ADC Usman Shugaba suka isa gidan Tunde.

Sabiu Yusuf wanda aka fi sani da Tunde, na zama a gida mai lamba 8 da ke Pilot Gate a fadar shugaban kasar.

Harbi a Aso Rock: An sauya wa dogarai 20 na Buhari wurin aiki
Harbi a Aso Rock: An sauya wa dogarai 20 na Buhari wurin aiki. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Me kika taba yi don inganta rayuwar yara- 'Yan Najeriya sun caccaki Aisha Buhari

An tsare dogaran uwargidan gwamnan a ranar Juma'a amma an sakesu a ranar Litinin.

Wata majiya ta sanar da The Punch cewa an sallami dogaran a ranar Laraba bayan shugaba Buhari ya duba bayanin lamarin, tare da duba karantsayen tsaro da aka samu a jihar Kebbi a ranar 13 ga watan Maris na 2020.

Jami'in ya ce, "A kalla dogarai 20 aka mayar wajen fadar shugaban kasar sakamakon abinda ya faru a fadar da kuma na baya.

"Wannan ya hada da abinda ya faru a jihar Kebbi yayin da wani yayi yunkurin cukuikuiyar shugaban kasar yayin da yake daukar hoto da gwamnan jihar Kebbi tare da wasu jiga-jigai."

Buhari ya ziyarci Kebbi don bude gasar kamun kifi ta Argungun, yayin da wani mutum mai suna Mohammed Gundarre ya yi hanzarin kai wa shugaban kasar damka.

Daga bisani, Gudarre ya yi bayanin cewa ya so yin hannu da shugaban kasar tare da tabbatar da cewa bai so cutar da shugaban kasar ba kuma bai yi tsammanin hakan zai kawo kalubale ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel