Wakata ta taba hana auren dole tare da ceton rai - Nura M. Inuwa

Wakata ta taba hana auren dole tare da ceton rai - Nura M. Inuwa

Fitaccen mawakin Hausa wanda yake daya daga cikin mawakan zamani kuma shahararre a kasar Hausa, Nura M Inuwa ya samu zantawa da BBC a shafin Instagram da Facebook.

Shahararren mawakin soyayyar ya sanar da cewa ya fara waka ne a 2007 kuma da wakar siyasa ya fara.

Kamar yadda Nura M Inuwa ya sanar, yanzu waka ta zame masa sana'a kuma hanyar gyara barna idan ta kunno kai a al'umma.

A cewar fitaccen mawakin, wakokinsa masu tarin yawa sun kawo sauyi. Akwai wakarsa mai take 'Ga Wuri Ga Waina' wacce ya yi magana a kan makomar duk wanda ya kashe kansa.

A sakamakon wannan wakar, "An samu wadanda suka kira ni tare da shaida min cewa nayi ceto. Yarinya ce ta so kashe kanta amma bayan jin wannan wakar sai ta fasa."

Mawakin ya kara da cewa wakarsa ta Tambihi ta yi sanadin fasa auren dole. Wani mahaifi ya yi yunkurin yi wa diyarsa auren dole amma jin wannan wakar yasa ya hakura.

Hakazalika, a wata wakar mawakin mai suna 'Dafin So' wacce ya yi maganganu masu tarin yawa, wani magidanci ya kirasa inda ya shaida masa cewa har yayi fushi da matarsa amma jin wakar yasa ya bita suka sasanta.

Wakata ta taba hana auren dole da ceton rai - Nura M. Inuwa
Wakata ta taba hana auren dole da ceton rai - Nura M. Inuwa. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

KU KARANTA: Yadda budurwa ta mutu a dakin saurayi (Hotuna)

Fitaccen mawakin ya bayyana cewa duk cikin wakoki, ya fi son wakar soayyaya saboda babu abinda ya fi soyayya dadi a rayuwa.

Mawakin ya ce ya yi wakoki masu tarin yawa amma bakandamiyarsa ita ce wakar 'Rigar Aro' da yayi.

A yayin da aka tambayesa abinda yasa ba a cika ganinsa a fina-finai ba, sai yace "Ni mutum ne mai son layi daya in tsaya a kansa tare da kwarewa a kai. Hakan yasa bana ra'ayin fim".

A wata hira ta daban, daga cikin sanannun jarumai maza na Kannywood kuma mawaki a kasar nan, Yakubu Mohammed, ya ce har gobe yana nan daram a jam'iyyar PDP.

Yakubu Mohammed ya sanar da hakan ne yayin hirar da yayi da BBC a shafinsa na Instagram kai tsaye a ranar Laraba.

Jarumin ya taba batutuwa da dama da suka shafi manyan nasarorin da ya samu a fannin fina-finan da yayi da wakokinsa tare da alakarsa da abokansa na sana'a.

Jarumi Yakubu Mohammed ya tabbatar da cewa tun fara siyasarsa, jam'iyyar PDP yake goyon baya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng