Handama: EFCC ta gurfanar da mataimakin kakakin majalisa da magatakarda

Handama: EFCC ta gurfanar da mataimakin kakakin majalisa da magatakarda

Hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ta gurfanar da mataimakin kakakin majalisar jihar Binuwai, Christopher Adaji da magatakardar majalisar, Torese Agena.

Sun gurfana a gaban Mai shari'a S. O. Itodo a ranar Laraba a gaban wata babbar kotu da ke garin Makurdi a jihar Binuwai a kan damfarar kudi har N5,040,950, jaridar Daily Nigerian ta wallafa.

Kamar yadda takardar da ta fito daga shugaban fannin yada labarai na hukumar, Dele Oyewale, ya ce wadanda ake zargin an gurfanar da su ne a kan laifukan hada kai wurin cuta, cin hanci, cin amana da amfani da kujerarsu ba ta yadda ya dace ba.

Amma kuma, dukkansu basu amsa laifukan da ake zarginsu ba bayan an karanto musu.

Daya daga cikin tuhumar ta ce: "A ranar 18 ga watan Oktoban 2019, Torese Agena a matsayinsa na magatakardan majalisar jihar Binuwai, ya yi amfani da kujerarsa wurin karbar N200,000 a matsayin cin hanci.

"Ya karba kudin daga High Profile Investment Nigeria Limited da sunan gwamnatin jihar Binuwai. Hakan ya ci karo da sashi na 19 na dokokin ICPC na 2000 kuma abun hukuntawa."

Handama: EFCC ta gurfanar da kakakin majalisa da mataimakinsa
Handama: EFCC ta gurfanar da kakakin majalisa da mataimakinsa. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda budurwa ta mutu a dakin saurayi (Hotuna)

Laifi na biyu an karanto shi kamar haka: "Cewa Christopher Adaji, a ranar 8 zuwa 14 ga watan Nuwamban 2019 ya karba kudi N4,840,950 wanda aka cirewa 'yan majalisar don zuwa ziyara turai.

"Wannan laifin ya ci karo da sashi na 22, sakin layi na biyar na dokokin ICPC na 2000."

Bayan sun musanta aikata laifin, lauyan masu gabatar da kara, G. G. Chia-Yakua, ya bukaci kotun da ta saka wata rana don sake shari'ar.

Ya kara da bukatar kotun da ta adana wadanda ake zargin a gidan gyaran hali.

Amma kuma lauyan wadanda ake kara ya bukaci kotun da ta bada belin wadanda yake karewa. Ya kara da cewa za su gurafana a gaban kotun a duk lokacin da ta bukata.

Mai shari'a Itodo ya bada belinsu tare da dage shari'ar zuwa ranakun 6, 7 da 8 ga watan Yulin 2020:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel