Kwarankwasa ta hallaka jami'an FRSC 3 a Ogun

Kwarankwasa ta hallaka jami'an FRSC 3 a Ogun

Mun samu cewa, kwarankwatsa ta fado kan wasu jami'an Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) su uku, sun mutu murus a jihar Ogun da ke Kudancin Najeriya.

Jami'an da ibtila'in ya ritsa da su suna bakin aiki ne lokacin da lamarin ya riske su ranar Laraba a garin Ilese da ke karamar hukumar Ijebu ta Arewa maso Gabas.

Wannan tsautsayi kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito ya auku ne da misalin karfe 10.00 na safiya yayin saukar yayyafi na ruwan sama a yankin tsohuwar tollgate da ke Ijebu-Ode.

An ruwaito cewa, kwarakwatsa ta fado kan jami'an uku yayin da suke shirye-shiryen gudanar da faretin su na safiya kamar yadda suka saba.

Kawo yanzu babu wani rahoto da Hukumar FRSC ta fitar dangane da aukuwar ibtila'in, sai dai wani jami'inta da ya bukaci a sakaya sunansa, ya tseguntawa manema labarai yadda ta kasance.

Kwarankwasa ta hallaka jami'an FRSC 3 a Ogun
Kwarankwasa ta hallaka jami'an FRSC 3 a Ogun
Asali: Facebook

Babban jami'in hukumar ya ce akwai kimanin ma'aikata 12 yayin da lamarin ya auku, inda nan ta ke mai yankan kauna ta yi wa mutum uku lullubi da bargonta.

Yayin da aka tuntubi jami'ar hulda da al'umma ta Hukumar FRSC reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ta tabbatar da aukuwar lamarin, amma daga nan ba ta kara komai a kan hakan ba.

Sai dai Okpe ta yi alkawarin waiwayar manema labarai daga baya domin yi musu karin bayani dangane da lamarin.

KARANTA KUMA: Jiragen Sojoji sun yi wa mayakan Boko Haram ruwan wuta a garin Maloma

Ta bayyana cewa, sai bayan Kwamandan rukunin jami'an da suka riga mu gidan gaskiya ya tattaro dukkanin rahoton yadda ta kasance kafin ta iya cewa komai a kan lamarin.

Legit.ng ta ruwaito cewa, ana yawan samun aukuwar wannan ibtila'i a lokutan damina, inda a bara akalla kimanin shanu 36 na wani makiyayi sun halaka yayin da tsawa da fada kansu.

Wannan ibtila'i ya auku ne a watan Satumba na shekarar da ta gabata a yankin Ijare na karamar hukumar Ifedore ta jihar Ondo a Kudancin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel