Fayose ya bayyana abinda ya haifarwa da jam'iyyar APC rikici

Fayose ya bayyana abinda ya haifarwa da jam'iyyar APC rikici

Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya ce jam'iyyar APC mai mulki ta fada cikin rigingimu ne saboda Allah yana fushi da jam'iyyar.

Jam'iyyar APC ta na fama da rigingimu kala biyu; rikicin zaben fidda dan takarar gwamnan jihar Edo da tabbatar da dakatar da shugabanta na kasa, Adams Oshimhole, da kotun daukaka kara ta yi.

Bayan APC ta sanar da korar takararsa, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya sanar da yin murabus daga zama mamba a jam'iyyar.

Sa'o'i kadan bayan ya sanar da barin jam'iyyar APC, wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da dakatar da Oshiomhole daga shugabancin jam'iyyar APC.

Lanre Issa-Onilu, sakataren yada labaran jam'iyyar APC, ya sanar da cewa kwamitin gudanarwa na jam'iyya (NWC) ya damkawa Abiola Ajimobi, rikon kwaryar shugabancin jam'iyyar APC.

Kafin nadinsa a matsayin shugaban rikon kwarya, Ajimobi, tsohon gwamnan jihar Oyo, ya kasance mataimakin shugaban jam'iyyar APC na shiyyar kudu maso yamma.

Duk da Ajimobi bashi da lafiya, ya na killace sakamakon kamuwa da kwayar cutar korona, kakakinsa, Bola Tunji, ya sanar da cewa tsohon gwamna ya bukaci mambobin jam'iyyar su zauna lafiya da juna.

Sai dai, hakan bai hana Victor Giadom, mataimakin sakataren jam'iyya, ya fito ya bayyana kansa a matsayin shugaban APC ba, tare da sanar da soke hukuncin korar takarar Obaseki.

Fayose ya bayyana abinda ya haifarwa da jam'iyyar APC rikici
Ayo Fayose
Asali: UGC

Amma, bayan mambobin NWC sun kada kuri'a yayin taron gaggawar da suka kira, sun yi watsi da ikirarin Giadom tare da jaddada shugabancin Ajimobi.

Kazalika, NWC ya amince Hilliard Eta, mataimakin shugaba na yankin kudu maso kudu, ya zama shugaba amadadin Ajimobi wanda ke zaman jinyar cutar korona.

DUBA WANNAN: An kori janar a rundunar sojin Najeriya 'babu girma, babu arziki'

A cikin wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Fayose ya bayyana cewa; "APC ta fada rikici ne saboda Allah ya na fushi da jam'iyyar a kan take hakkin 'yan Najeriya, daurewa magudin zabe gindi da kuma kawar da kai a yayin da ake kashe dubban jama'a.

"Allah ba zai taba yin farin ciki da jam'iyyar da ta gaza yin komai a kan zubar da jinin jama'a da aikata fyade ga kananan yara da kuma lalatawa jama'a harkokin kasuwancinsu ba.

"Kazalika, Allah ba zai yi farin ciki da jam'iyya irin APC ba; saboda rashin sanin makamar aiki da rashin hangen nesa na gwamnatin jam'iyyar ya sa an ciyo bashin da jikoki da tattaba kunne za su dade basu gama biya ba.

"Ta yaya Allah zai yi farin ciki da jam'iyyar APC bayan ta goyi bayan magudin zabe a shekarar 2015 da kuma wanda aka tafka a 'yan kwanakin baya bayan nan a jihohin Kogi da Bayelsa?.

"Tabbas, Allah ba zai barsu ba, dole gidan jam'iyyar APC da aka gina da tubalin karya da jinin 'yan Najeriya ya rushe."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng