Yadda budurwa ta mutu a dakin saurayi (Hotuna)

Yadda budurwa ta mutu a dakin saurayi (Hotuna)

Dalibar jami'ar tarayya da ke Oye Ekiti a jihar Ekiti mai suna Faderera Oloyede ta rasu a dakin saurayinta mai suna Ayo Maliki.

Budurwar ta rasu a ranar Talata, 16 ga watan Yunin 2020.

Faderera daliba ce da ke aji uku inda take karantar lissafi. Ta ziyarci saurayinta da ke yankin Koko na Iree a jihar Osun tare da wata kawarta mai suna Kemisola Adewusi.

Kemisola Adewusi daliba ce a jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Kamar yadda wata majiya ta sanar, Maliki ya dafa wa bakinsa shinkafa amma yayin da Oloyede ke ci sai ta fara korafin ciwon ciki.

Babu dadewa ta fara amai. A take kuwa ta ce ga garinku duk da yunkurin ceto rayuwarta da Maliki tare da sauran suka yi.

"Sun yi kokarin ceto rayuwarta amma sai ta mutu yayin da take korafin ciwon ciki," wani makwabcinsu da ya bukaci a boye sunansa ya sanar.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola ta ce ana bincike a kan al'amarin.

Ta bayyana cewa kawar da ta yi wa mamaciyar rakiya a halin yanzu tana tsare.

"A lokacin da aka kira mu, mun je mun dauka gawar inda muka mika ta ma'adanar gawawwaki da ke Osogbo.

"Sashen binciken laifuka na musamman na jihar ya karba al'amarin don bincike." Opalola tace.

Yadda budurwa ta mutu a dakin saurayi (Hotuna)
Yadda budurwa ta mutu a dakin saurayi (Hotuna). Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Harbi a Aso Rock: An sauyawa masu tsaron Aisha Buhari wurin aiki

Yadda budurwa ta mutu a dakin saurayi (Hotuna)
Yadda budurwa ta mutu a dakin saurayi (Hotuna). Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

Har ila yau, matashiya mai shekaru 19 a yankin Ndola da ke Zambia ta tsere daga gidan mijinta saboda tsananin bukatar jima'i da mijinta ke yi wanda hakan ke zarcewa tsawon dare.

Matar auren da ke Mushili, ta yi bayanin hakan a gaban wata kotu da ke Kabushi. Ta ce ta tsere daga gidan mijinta saboda ya fiye bukata.

Yana ji mata ciwo kuma baya gamsuwa da wuri. Bata bacci don sukan kwashe tsawon dare suna aiki daya.

Charity ta ce mijinta na kwanciya da ita duk dare sannan yana bukatar samfur kala-kala. Hatta lokutan da take al'ada baya sassauta mata.

Ta yi bayanin cewa ba za ta iya jure irin wannan rayuwar ba da zai dinga kwanciya da ita kowacce rana, don haka ta tsere don neman mafita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel