Edo 2020: Akwai yiwuwar Obaseki ya koma APC - Kakakinsa

Edo 2020: Akwai yiwuwar Obaseki ya koma APC - Kakakinsa

Da hukuncin kotun daukaka kara na jaddada dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar APC, akwai yuwuwar gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya koma jam'iyyar, kakakinsa ya sanar.

A ranar Talata, Obaseki ya sanar da barin jam'iyyar APC bayan ganawar da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasan da ke Abuja.

Hakazalika, mataimakin Obaseki, Philip Shaibu, ya bar jam'iyyar APC. An ga hotunansa a gidan gwamnatin tare da bidiyo inda yake cire tutar APC daga ofishinsa.

Gwamnan ya bar jam'iyyar ne sakamakon hanasa shiga sahun masu bukatar tikitin takarar kujerar gwamnan jihar a 2020.

Bayan hukuncin kotun koli a kan Oshiomhole, APC ta nada mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, Abiola Ajimobi, tsohon gwamnan jihar Oyo a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa.

Amma kuma, Ajimobi na kwance a asibiti sakamakon kamuwa da yayi da cutar korona.

Jaridar Premium Times ta samu zantawa da kakakin Gwamna Obaseki, Crusoe Osagie, ta tambayesa ko gwamnan na da burin komawa jam'iyyar APC.

Edo 2020: Akwai yuwuwar Obaseki ya koma APC - Kakakinsa
Edo 2020: Akwai yuwuwar Obaseki ya koma APC - Kakakinsa. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Bayan haihuwar 'yan uku, matashiya mai shekaru 19 ta riga mu gidan gaskiya

"A gaskiya ban yi magana da uban gidana ba a kan hakan. Amma ban ga wani abu ba daidai ba idan yayi hakan," Osagie ya sanar a ranar Laraba.

"Da dukkan niyya, idan ka dubi dalilin da yasa gwamnan ya bar jam'iyyar, duk ya dogara ne da Oshiomhole da kuma yadda yake tafiyar da jam'iyyar," yace.

"Bayan kotu ta dakatar da Oshiomhole, akwai yiwuwar ya dawo ballantana da bai koma wata jam'iyyar ba," ya kara da cewa.

Osagie ya ce gwamnan bai taba samun wata matsala da jam'iyyar APC ba.

A yayin da jaridar Premium Times ta tambaya Osagie ko ubangidansa baya tunanin koda ya dawo ya rasa tikitin tunda ba Oshiomhole bane kadai ya yanke hukuncin farko.

Osagie ya ce, "Oshiomhole shi kadai ne. Nan da kankanin lokaci za ka ga masu ikirarin biyayya ga Oshiomhole duk babu su."

Osagie ya ce kotun daukaka kara ta dogara da korafin da aka kai dangane da Oshiomhole ne tun daga gundumarsa a watanni bakwai da suka gabata.

"Wannan na nuna cewa, duk abinda Oshiomhole yayi da kansa yayi kuma hatta gundumarsa basu aminta da shi ba," ya kara da cewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel