Har ila yau: Wata sabuwar zanga -zanga ta balle a jihar Benuwe

Har ila yau: Wata sabuwar zanga -zanga ta balle a jihar Benuwe

- Kungiyoyi da dama a najeriya na cigaba da bayyana damuwarsu a kan samun yawaitar matsalar aikata fyade

- A jihar Benuwe, kungiyoyi da dama sun shiga zanga - zangar nuna rashin jin dadinsu a kan yawaitar karuwar aikata fyade a jihar

- Masu zanga - zangar sun bayyana cewa an aikata laifi fyade guda 8 a cikin sati guda a yankin Otukpo kadai

Dumbin masu mambobin kungiyoyi sun mamaye yankin Otukpo a jihar Benuwe domin gudanar da zanga - zangar nuna jin rashin jin dadinsu a kan samun yawaitar matsalar aikata fyade ga 'ya'ya mata a yankin da fadin jihar.

An shirya zanga - zangar ne a karkashin gamayyar kungiyoyin da ke yaki da aikata fyade a jihar Benuwe (BeCare).

Jagororin zanga - zangar sun bayyana damuwarsu a kan yadda aka samu matsalar aikata fyade har 8 a cikin mako guda a iya yankin Otukpo kadai.

Da yake magana da manema labarai, jagoran masu zanga - zangar, Prince Yemi Itodo, ya ce sun shirya zanga-zangar ta lumana ne domin wayar da kai a kan illolin da ke tattareda aikata fyade da kuma neman a kawo karshen matsalar.

Har ila yau: Wata sabuwar zanga -zanga ta balle a jihar Benuwe
Masu zanga -zanga a jihar Benuwe
Asali: Facebook

A kalmomin Itodo: "mun shirya wannan zanga - zanga domin nunawa masu jin dadin aikata fyade cewa abinda suke yi ba daidai bane, lokaci ya yi da ya kamata su sauya, su nemi sabuwar rayuwa.

DUBA WANNAN: Katsina: Buhari ya aika sako ga masu zanga - zanga a kan rashin tsaro

"A cikin mako daya kawai, an yi wa yara mata 8 fyade a sassan kananan hukumomin jihar Benuwe, amma mutum 3 ne kacal a hannun rundunar 'yan sanda."

Masu zanga - zangar sun bi ta cikin garin Otukpo zuwa ofishin rundunar 'yan sanda, sannan suka bulle ta gaban sakatariyar karamar hukuma zuwa ta gaban fadar babban sarkin masarautar Otukpo/Ohimini.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel